1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BUKUKUWAN KARBAR SABBIN KASASHE GOMA A KUNGIYYAR EU.

May 1, 2004

HOTON DAYA DAGA CIKIN SABBIN KASASHE GOMA DA AKA KARBA A CIKIN KUNGIYYAR TA EU.

https://p.dw.com/p/Bvk4
Hoto: AP

Kamar yadda kuka ji a labaran duniya a tun daren jiya sabar din ne tsoffin kasashe na kungiyyar ta Eu da kuma sabbin kasashe goma ke gudanar da bukukuwa iri daban daban na murnan wan nan abin tarihi daya wanzu a tsawon shekaru da dama da suka gabata.

Wadan nan sabbin kasashe dai sun hadar da kasashe takwas da suka fito daga yankin kasaashe na kwaminisanci da suka hada da Kasar Poland da kasar czech da Slovenia da Hungry da Slovenia da Estonia da Latvia da kuma Lithunia. Ragowar kasashe biyun kuma sun hada da kasar Malta da kuma yankin Cyprus na kasar Girka.

Sakamakon wan nan sabon ci gaba da aka samu a yanzu haka kungiyyar ta Eu nada mambobi 25 a maimakon guda goma sha biyar da take dasu a baya.

A lokacin wadan nan bukukuwa rahotanni sun shaidar da cewa da yawa daga cikin mutanen wadan nan kasashe sun gudanar da kide kide da raye raye iri daban daban a hannu daya kuma da gudanar da wasan harba wuta sama dake dauki da launi kala kala,abin dai abin ban sha,awa sai wanda ya gani.

Bugu da kari a lokacin wadan nan bukukuwa na murna a kasar Ireland wacce ke rike da shugabancin karba karba na kungiyyar ta Eu an gudanar da wake wake iri daban daban kuma cikin harsuna daban daban da suka fito daga wadan nan kasashwe goma.

A lokacin da yake jawabi lokacin gudanar da wan nan biki mai dinbim tarihi shugaban hukumar zartarwa na kungiyyar ta Eu Romano Prodi nuna farin cikan sa yayi a maimakon hukumar zartartwar ta Eu da karbar wadan nan sabbin kasashe guda goma goma a cikin kungiyyar ta Eu.

Romano Prodi yaci gaba da cewa a nan gaba yana sa ran cewa kungiyyar ta eu zata kara shigar da wasu kasashe a cikin ta.

Sakamakon karbar wadan nan kasashe goma Mr Romano Prodi ya tabbatar da cewa yanzu haka mutanen dake cikin wadan nan kasashe na Eu 25 sun zamo kasa daya alumma daya,a don haka abin da yare shine na a hada karfi da karfe guri guda don tunkarar lalubalen dake gaba.

Haka suma shugabannin kasashen Jamus wato Gerhard Schroder da faraministan kasar Czech vladimir Spidla da kuma na kasar Poland sun hadu a wani gari mai suna Zittau dake karshen iyakar kasar ta Jamus a daren jiya don gudanar da nasu bikin murnan shigowar sabbin kasashen goma cikin kungiyyar ta Eu.

Haka suma dubbannin mutane na wadan nan kasashe sun hadu a iyakokin kasashen don gudanar da nasu bukukuwan murnar wan nan rana ta yau asabar.

A waje daya kuma tsohun shugaban kasar Czech Vaclav Havel cewa yayi babu shakka shigowar wadan nan kasahe goma zai kara bunkasa kungiyyar ta Eu ta zama tana gogayya kafada da kafada da sauran takwarorin ta a duniya.

Bisa hakan ya bukaci daukacin mutanen kasar su dasu zama masu yiwa kungiyyar ta Eu fata na Alheri don samun cimma nasarar data sa a gaba.

Bayanai kuma daga kasar Hungry sun nunar da cewa bisa daukar wan nan rana ta yau da muhimmanci gwamnatin kasar ta bayar da sanarwar ciyar da mutanen kasar karin kumallon safe ne na yau asabar.

Su kuwa mutanen kasashe irin su Poland da Czech da kuma yanin Cprus na girka cewa sukayi mafarki ne da suka dade sunayi ya tabbata a wan nan rana ta yau asabar.

Ata bakin Wani dan yanin Cprus na kasar Girka mai suna Gajek cewa yayi shigar kasar su cikin kungiyyar Eu abune babba´da zai janyowa kasar su kima da daukaka a duniya musanmamma bisa laakari da irin kasashe dake cikin kungiyyar.

A yanzu haka dai bayanai sun shaidar da cewa a yayin da ake gudanar da wadan nan bukuwa a daya hannun kuma wasu na cike da hasashen yadda kungiyyar zata zamo a nan gaba musanmamma bisa irin kalubalen dake gaban ta,kamar su batun saye da sayarwa da ala,du da tattalin arziki da ire iren makaman tansu.

IBRAHIM SANI