Bukukuwan cikar Pakistan shekaru 60 da samun ´yancin ta | Labarai | DW | 14.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukukuwan cikar Pakistan shekaru 60 da samun ´yancin ta

A yau Pakistan ke gudanar bukukuwan cika shekaru 60 da samun ´yancinta daga kasar Birtaniya. A fadin kasar baki daya ana gudanar shagulgula na tunawa da raba yankin zuwa Pakisan mai rinjayen al´umar mulsulmi da Indiya mai rinjayen ´yan Hindu a shekarar 1947. a lokaci daya kuma an yi shiru na minti guda don tunawa da dubun dubatan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon tarzomar da aka yi a wancan lokaci. A cikin wani jawabi na ranar samun ´yanci shugaba Pervez Musharraf yayi kira ga ´yan Pakistan da su marawa masu sassaucin ra´ayi baya a zaben ´yan majalisar dokoki da ake sa ran gudanarwa a karshen wannan shekara. Musharraf dai na fuskantar mummunar adawa daga masu tsattauran ra´ayin Islama. A gobe Indiya makwabciyar Pakistan zata yi nata bukukuwan.