1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bukukuwan Azumin Ramadan

Muhimman bubukuwa na buɗa baki a lokutan Azumi

default

Ga musulmin Duniya da yake Ramadan na ɗaya daga cikin shika-shikan addinin musunlci, lokaci ne da ke da muhimmacin sosai ga dukkanin musulmin a Duniya baki daya. Idan lokkacin buɗa baki yayi ana shirya ire iren bukukuwan al'adun gargajiya. Birnin Berlin dake dauke da mafi ya yawan al'umman musulmi a nan Jamus ana gudanar da ire iren wadanan bukukuwa a wurare dabam dabam daga yanzu har sha biyu ga wata mai kamawa.

Shekaru 106 ke nan da kafa gidan tarihi na Islamic Art in Berlin. Yanzu kam a buɗe yake ga jama'a baya ga ganin da suke yi a hotuna da kuma  tallarsa a kwalin taba. Yanzu addinin musulunci ya zamo ruwan dare gama gari a ƙasar Jamus da ke ɗauke da musulmi kusan miliyan huɗu a yayin da suma suka bi sahun yan uwan musulmi suke guddanar da azumin amadan na wannan shekara.

Marokko Ramadan

I

A cewar Tamer Ergun haifaffen birnin Instanbul. Tun lokacin da yake ɗan karaminsa ne ya san cewar Ramadan na ɗaya daga cikin shika shikan addinin musulunci.

"Lokaci ne da ya kamata mutun yayi sulhu da kansa kuma ya nemi zaman lafiya da yan´uwansa"

Ya kara da cewar a  cikin Alkur'ani mai girma akwai inda ke nuna cewar a cikin wata na tara na kalandar musulunci  ya kamata duk musulmi ya rike bakinsa daga fitowar rana har faɗuwarsa. Ya mayar da hankali ga bauta wa Ubangijin dama sulhu tsakanin al'umma kuma don hakan na da muhimmaci yasa nake farin cikin haɗuwa da abokai dama ´yan'uwan a koda yaushe domin shan ruwa tare kana mu ci gaba da bukuwakuwan da muka saba yi. Haka ma lamarin yake a ƙasar Siriya, ko Turkiya har da su Birtaniya, Paris da ma Berlin.

A cewar shugaba mai kula da gidan tarihin ta Islamic Art in Berlin Stefan Weber

Cudanya da sauran jamaa baya nuna cewar kamata su matsa wa kansu ko kuma su yi watsi da aladunsu

kana su ci gaba da bukukuwan Krismeti kamar yadda wasu musulmi ke yi.

Marokko Ramadan

`Da yake wannan batu sai da ci gaba yake kamata yayi a magance wannan batun tun yanzu ta hanyar shirya wasanin rera wakoki, al´adun gargajiyan da tare da na zamani da musulmi suka amince da shi a cewar Anna Mechelhoff shugaban kuka da shirye shirye na kampanin  Aladu ta Pinraha

"Kwarai kuwa za'a iya haɗa ɓangaren al'adu a ɗayan hannu kuma a yi anfani da yankuna, daga ƙasar China zuwa Siriya, yammacin Afirka, Turkiya  haɗe da Berlin. Hanyoyin ke nan da masu aikin zane-zane ke anfani da shi kuma suke samun bunkasa." 

Mawallafiya: Ramatu Abubakar Mahmud

Edita:     Zainab Mohammed Abubakar