Bukin tunawa da bayi a Faransa | Labarai | DW | 10.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukin tunawa da bayi a Faransa

A karon farko kasar Faransa ta gudanar da bikin ranar yaki da cinikin bayi don tunawa tare da girmama wadanda wannan ciniki ya shafa, yau shekaru 158 da haramta wannan aiki a duniya. Daga karni na 16 zuwa shekarar 1848 jiragen ruwan Faransa musamman daga biranen Bordeaux da Nantes sun yi jigilar bayi kimanin miliyan 1.2 daga Afirka zuwa Amirka da Caribean. A lokacin da yake jawabi a gun bikin da aka yi a birnin Paris shugaba Jacques Chirac ya ce dole ne a girmama miliyoyin mutanen da wannan ta´asa ta rutsa da su. To sai dai masu suka sun ce bukin tunawan bai dace da sabon shirin doka ga baki wanda aka kirkiro bayan tarzomar da matasa suka yi a bara ba. Shirin dokar zai saukaka korar baki tare da kawo cikas ga hade kan iyali. Kungiyar kwadago ta duniya ta ce sama da mutane miliyan 12 a ke aiki irin na bauta musamman a nahiyar Asiya, Afirka, Latun Amirka da ma wasu kasashen Turai.