1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukin samun shekaru 17 da sake haɗewar Jamus

A yau tarayyar Jamus ke bukin cika shekaru 17 da sake hade yankin gabas wanda ya taba zama karkashin tsarin kwaminis da yammacin kasar. A daidai lokacin da ake wannan buki a yau batun harajin nan da ake yiwa lakabi da harajin zumunci wanda ma´aikata ke biya don sake gina gabashin kasar shi ya dauki hankalin jama´a. Ana dai yawaita yin kira da a soke wannan haraji na kashi 5.5 cikin 100 na albashin kowane ma´aikaci a nan Jamus. Daukacin ´yan siyasa na bangaren adawa sun goyi da bayan kawo karshen wannan haraji ko kuma a rage to amma ´ya´yan jam´iyar SPD na son a ci-gaba da biya. A cikin shekarun bayan nan an samu kwararar matasa daga gabashin zuwa yamacin kasar ta Jamus. Bincike yayi nuni da cewa kashi daya cikin 3 na mata matasa na shirin barin yankin gabashin suna masu cewa ba sa son tsarin rayuwa na yankin.