1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin Sallar Layya

November 16, 2010

Al'ummar Musulmin Nijeriya ta bi sahun takwarorin ta na Duniya wajen shagalin Sallar Layya

https://p.dw.com/p/QAQX
Wani Bafalasɗine ɗauke da rago a sansanin 'yan gudun hijra da ke RafahHoto: AP

Yau ne a al'ummomin Musulmi a ƙasashen Duniya daban daban ke shagulgulan Sallar layya, bayan da a jiya Litinin mahajjata kimanin miliyan uku daga ƙasashe daban daban na duniya, su ma su ka yi hawan arfa da ke matsayin ƙololuwar aikin hajji.

Rahotanni daga Tarayyar Najeriya sun ruwaito cewar, a bana raguna sun yi matuƙar tsada, ta yadda layya ta gagari mai ƙaramin ƙarfi. Tunda farko a jawabin da Wazirin Sokoto Dakta Usman Junaidu ya gabatarwa al'ummar musulmin Nijeriya a madadin Sarkin Musulmi Dakta Muhammad Sa'ad Abubakar da ke yin aikin hajjin ya taya su murnar Sallar Layyar ce, tare da yi musu fatan Allah ya karɓi ibadar su.

Sai dai kuma a jamhuriyyar Nijar hukumomin ƙasar sun sanar da gobe Laraba ce idan Allah ya kaimu a matsayin ranar shagulgulan Sallar Layyar. Baya ga Nijar ɗin ma a can ƙasar Morokko sai gobe ne take Sallah.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammed Abubakar