1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukin sake haɗewar gabashi da yammacin Jamus

Yau shagulgulan bukin sake haɗewar Jamus a matsayin ƙasa guda ke kai ƙololuwarsu

default

Iran Atom 5+1 Symbol

A halin da ake cikin yanzu ana nan ana gudanar da shagulgula da suka haɗa da kiɗe-kiɗe da raye-raye a biranen Berlin da Bremen da ma sauran biranen Jamus a dangane da bukin cika shekaru 20 na sake haɗewar gabashi da yammacin ƙasar. A ranar 3 ga watan Oktoban 1990 ne dai ɓangarorin biyu suka sake haɗewa a hukumance bayan rarrabuwar kawuna na kusan shekaru 40. Kantagar Berlin da ta raba Jamus gida biyu a wancan lokaci, an wargajeta ne watanni 11 gabanin sake samun haɗin kai tsakanin gabashi da yammacin Jamus. Tun daga wannan lokaci ne kuma aka tsai da ranar 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu a faɗin Jamus. A wannan shekara birnin Bremen ne ya karɓi matsayin karɓa-karɓa na jagorantar bukuwan haɗin kan. Mahukunta wannan birni sun gina wata katanga makamanciyar ta Berlin a dandalin wata kasuwa domin nuna tarihin rarrabuwar kawuna da Jamus ta fuskanta. Ana sa rai cewa shugabar gwamnati, Angela Merkel za ta yi jawabi a dangane da wannan buki a birnin na Bremen a yau ɗin nan.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Mohammad Nasiru Awal