1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin rantsar da shugaban kasar Congo

December 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuYy

A yaune ake bukin rantsar da zababben shugaban JDC a birnin Kinshasa,dake zama fadar gwamnati.Joseph kabila mutumin farko da aka zaba a matsayin shugaban kasa a zaben farko na Democradiyya ,a wannan kasa dake tsakiyar Afrika a sama da shekaru 40 da suka gabata.Dubbannin magoya bayansa nedai sukayi dafifi a wajen harabar Kotun da ake gudanar da wannan buki na rantsar dashi.Wannan sabon yanayi na Democradiyya a Congon dai,ya fuskanci tashe tashen hankula,kana a makonni biyu da suka gabata ne kuma yan adawa suka cinnawa harabar wannan kotu wuta.A hsalin da ake ciki yanzu dai dakarun Uganda sun sanar dacewa sama da yan JDC dubu 12 suka tsere ta kann iyakokin kasashen biyu,zuwa kudancin Ugandan,sakamakon cigaban fada tsakanin dakarun Congon dana yan adawa.