1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin rantsar da shugaban Afrika ta kudu.

April 27, 2004

Bukin cika shekaru 10 da kawar da mulkin nuna wariyar launin fata a Afrika ta kudu,da rantsar da Thabo Mbeki a karo na biyu.

https://p.dw.com/p/BvkG
Thabo Mbeki na hannu da alummar kasar sa,bayan rantsar dashi a karo na biyu.
Thabo Mbeki na hannu da alummar kasar sa,bayan rantsar dashi a karo na biyu.Hoto: AP

Yanu ne akayi bukin rantsar da shugaba Thabo Mbeki na kasar Afrika ta kudu a matsayin shugaban kasa a karo na biyu,ayayinda kuma a daya hannu alummar kasar ke bukin cika shekaru 10 da kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata a wannan kasa.

A jawabinsa bayan rantsarwa ,shugaba Mbeki yace yau ne Afrika ta kudu ta shiga wani karni na mulkin Democradiyya,wanda ke tabbatar dacewa yan Afrika zasu iya shawo kann matsalolinsu da kansu,ba tare da tsoma bakin kasashen ketare ba.Yace an dauki shekaru da dama ana gwagwarmaya,amma ayayanzu haka Afrika na mai zama wurin fata na kasancewa abun koyi ga sauran nahiyoyi.An gudanar da bukin ne a Dandalin fadar gwamnatin kasar dake Pretoria,shekaru 10 daidai da rantsar da Nelson Mandela a wannan cibiya,bayan kawar da mulkin nuna wariyar launin fata.

Mai shekaru 61 da haihuwa,Mbeki ya jagoranci Jammiyar ANC mai mulki zuwa nasaran lashe zabe da kusan kashi 70 daga cikin 100 na yawan kuriu da aka kada ranar 14 ga watan Afrilun daya gabata,wanda ya kasance karo na uku da akayi zabe a karkashin mulkin democradiyya bayan kawar da mulkin nuna wariyar Alumma a wannan kasa.

Mai dakinsa Zanele,ta mara masa baya zuwa dandalin wannan buki ,inda ya samu kyakkyawan maraba daga kungiyoyin mawaka na zulu,yan choire tare da dubban mutane da suka halarci bukin na yau.Bugu da kari a matsayin darajawa da kuma girmamawa anyi harbin bindigogi sau 21 daga bangaren dakarun tsaron kasar da sukayi masa Paradi na musamman,banda jirgi kirar saukan ungulu da aka gabatar dauke da launin tutar Afrika ta kudun watau blue,yallo,ja ,fari koriya da baki.

A jawabinsa,shugaba thabo Mbeki ya tunatarwa alummar kasar shekarun nuna wariyar launin fata a wannan kasa,da kuma irin wahalhalu da bakaken fatar kasar suka fuskanta na wancan lokaci.yace a wannan lokacin idan aka haifi bakar fata tamkar annoba ce tazo wa wannan iyali,inda aka fuskanci kisangilla da fyede da tozartawa bakake mara misaltuwa,Ya kara dacewa a wancan lokacin ana amfani da bindigogi da tankunan yaki wajen kisan gilla wa duk wani baki dayayi yunkurin tada zaune tsaye na farar fata,wadanda suke da wuka da naman mulkin kasar a wancan lokaci.Mbeki yace da zaayi ramuwar gayya,amma amaimakon haka yanzu ana samun hadin kai tsakanin farare da bakake a Afrika ta kudu,kuma yanzu haka bangarorin biyu sun gano cewa kowane zai iya dogaro da danuwansa.

Daruruwan sarakunan gargajiya ,Ministoci da shugabannin kasashen afrika sun samu halartan wannan buki.Cikin shugabannin na Afrika harda da shugaban Zimbabwe Robert Mugabe,wanda ya samu kyakkyawar maraba daga mahalarta wannan buki, alokacin daya iso domin daukan kujera.Bugu da kari tsohon shugaba Nelson Mandela na kasar ta Afrika ta kudu,shima ya samu kyakkyawar maraba daga alummomin kasar da suka halarci wannan gagarumin buki yau.

Mbekin dai a matsayin shi na kasancewa bakar fata na biyu daya shugabanci wannan kasa a shekaru 10 da suka gabata,yayi alkawarin samarda ayyukanyi wa jamaa,Rage talauci da kuma inganta fannin kiwon lafiya,tare da bawa mata yancin tofa albarkacin bakinsu cikin harkokin mulki daya shafi kasar.

Raye raye da wasannin kwaikwayo daya bayyana irin nasaran da Afrika ta kudun ta samu cikin shekaru 10 da suka gabata,ya karawa wannan buki armashi.Ayayinda da yammacin yau ne zaa shirya liyafa da wasanni na musamman wa manyan baki,a cibiyar aladu dake birnin na Pretoria,domin tunowa da yancin da bakaken kasar suka samu daga Farare marasa rinjaye.

Zainab AM Abubakar.