1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin rantsar da Shugaban ƙasar Rwanda

September 6, 2010

Paul Kagame yace lokaci yayi da ƙasashen Duniya zasu kyale Afirka tayi rawar gaban hantsinta, saboda bata bukatar wani Darasi

https://p.dw.com/p/P5YP
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaban ya bayyana haka  ne lokacin bikin rantsar da shi da aka yi, bayan ya sake lashe zaɓe da aka yi cikin watan Agusta da ya gabata.

Dubun dubatar jama'a ne suka halarci wannan bikin rantsarwa da aka yi a filin wasa na babban birnin ƙasar wato Kigali, baya ga shugabannin ƙasashen Afirka da dama da suma suka sami damar shaida wannan biki.

Bayan da ya karɓi rantsuwar kama aiki daga shugaban kotun kolin ƙasar, shugaba Kagame ya  shaidawa taron cewa ƙasashen yamma na sukar duk wani abin alheri da Afirka ta yi tare da ƙoƙari dora mata alhakin duk wani abu mara kyau da su suka jawo shi.

Yace a yanzu Al'ummar nahiyar Afirka ba sa bukatar koyan darasin da a ko da yaushe ake maimata musu, inda ya ba da misali da irin sukar da ya sha daga irin waɗannan ƙasashe da ƙungiyoyin kare hakkin bil adama, kan cewa ya nuna danniya a zaɓen da aka yi wanda ya samu nasara a ƙarshensa.

Mr. Paul Kagame ya jaddada cewa ƙasashen nahiyar Afirka zasu iya bunkasa kansu, ta hanyar samar da wadataccen abinci da inganta harkokin kasuwanci da zuba jari da kuma samar da ababen more rayuwa.

Ruanda Präsidentschaftswahl 2010 Afrika Kigali
Hoto: picture-alliance/dpa

Kagame ya samu nasarar lashe zaɓen da ya gudana a ƙasar a ranar 9 ga watan Agusta da kimani kaso 93 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa , bayan suka da gwamnatinsa ta sha akan hana manyan Jam'iyyun adawa shiga wannan zaɓe.

Ko da yake wannan ne karo na biyu da Mr. Kagame zai shugabanici ƙasar ta Rwanda, za a iya cewa shi ke jagorancita tun bayan kisan kiyashin da ya auku a 1994. Sannan ya taka rawa a gwamnatin da aka kafa bayan kisan kiyashin, in da ya rike mukaman mataimakin shugaban ƙasa da kuma ministan tsaron ƙasar.

 A baya dai Paul kagame ya sha yabo daga ƙasashen Turai bisa tsayuwar dakansa wajen inganta tattalin arzikin  Rwanda.

Daga cikin shugabanin ƙasashen da suka halarci bikin har da shugaban jamhuriyyar dimokaradiyyar Congo Joseph Kabila, wanda rahoton da Majalisar Ɗinkin  Duniya zata fitar a kan ƙasarsa ya zargi Dakarun ƙasar Rwanda da hannu a kisan kiyashin da ya auku tsakani 1996 zuwa 1998.

Sai dai kuma gwamnatin Rwanda ta yi watsi da waɗannan tuhume tuhume tare da barazanar janye dakarun ƙasar dake aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan, muddin Majalisar Ɗunkin Duniya ta buga wannan rahoto.

Ruanda Präsidentschaftswahl 2010 Afrika Kigali
Hoto: picture-alliance/dpa

Sauran shugabannin ƙasashen Afirka da suka sami halarta bikin rantsuwar sun haɗa da Mwai Kibaki Na Kenya da Blaise Compaore na Burkina Faso da Fracoise bozize na jamhuriyar Afirka ta tsakiya da faure Gnassingbe na  Togo da kuma Thomas yayi Boni na ƙasar Benin.

Haka zalika akwai wakilan  ƙungiyar ƙasashen Afirka, sannan ƙasashen Algeria da Uganda Da Swaziland sun aike da  nasu wakilan.

An dai kawata wurare da dama a kasar da ado iri iri, yayin da shaguna da katunan dake babban birinin suka yiwa kofofinsu fentin tutar kasar wato shudi da rawaya da kore 

Mawallafiya: Halima Umar Sani

Edita:Zainab Mohammed Abubakar