Bukin ranar Ruwa ta majalisar dunkin duniya | Zamantakewa | DW | 22.03.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bukin ranar Ruwa ta majalisar dunkin duniya

22 ga watan maris na kowace shekara na mai zama ranar da aka kebe domin nazarin bukatar wadata jamaa da ruwa.

Ruwan sha mai tsabta

Ruwan sha mai tsabta

Acikin sheakarun 1990s,an sha gabatar da shirye shirye musamman ta kafofin yada labarai,wadanda ke gargadi dangane da muhimmancin ruwansha a harkokin siyasar yankin gabas ta tsakiya.

Gababbin nadinsa a matsayin sakatare general na mdd a shekarata 1991,tsohon ministan harkokin waje na kasar masar Boutros Boutros Ghali, yayi hasashen cewa wani bababn yaki da zaa fuskanta a yankin shine matsalar ruwa.Kuma alal hakika wannan hasashe na Boutros Ghali bai kasance karya ba,domin matasalar ruwa ta zame wata babbar damuwa dake kawo sabani tsakanin kasashen wannan yanki na gabas ta tsakiya.Kum kawo zuwa yanzu,bincike da aka gudanar yayi nuni dacewa matsalar ruwa da ake cigaba da fuskanta a wannan yanki ya zaman to abun damuwa matuka.

Sakamakon karuwan yawan mutane da kuma harkokin noma na zamani a sassa na duniya baki daya ,rabin karnin daya gabata ya samu karuwar bukatun na ruwa na kusan ninki uku.Rahotan da bankin duniya ya fitar a wannan wata da muke ciki na nuni dacewa,yankin gabas ta tsakiya yafi kowane yanki na duniya fuskantar matsalar karancin ruwa.

Adangane da wannan matsala nedai shugabannin gudanarwa na bankin duniya sukayi kira ga gwamnatocin dake yankin dasu sanya harkokin kula da ruwa ,cikin ayyaukan tattalin arzikinsu.

Mataimakiyar shugaban bankin duniya dake kula da yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afrika Daniela Gressani,ta jaddada bukatar mayar da hankali kan shawo kan matsaloli na karancin ruwa,fiye da wasu batutuwa .Domin inji ta ruwa nada alaka da manyan matutuwa da suka hadar da noma da kasuwanci da harkokin kudi da kuma farashin makamashi.

Masar dai na daya daga cikin kasashen dake fama da karancin ruwa,duk da kasancewar kogin Nile ,domin kashi 88 daga 100 na yawan ruwan da kasar keda shi,yana tafiya ne kan harkokin noman rani.To sai dai manazarta harkokin tattali na yankin sun nunar dacewa,sashin noma na masar din na bada gudummowan kasa da kashi 25 daga cikin dari kachal,na kudaden shiga da kasar take samu.

Sakamakon karancin ruwan sama da yankin gabas ta tsakiya ke fama dashi,kana bata da wani ruwan da take samu daga kasa,mafi yawan kasashen yankin na dogaro ne kan ruwan kogin Nile.Kasashe da dama na cin moriyar wannan kogi daga nahiyar Afrika,amma wadanda sukafi cin moriyarsa sune kasashen masar da sudan da habasha.To sai dai akwai kiraye kiraye dangane da bukatar daidaita yadda kasashe zasu rika cin moriyar wannan kogi na Nile,domin suma suna fuskantar karuwan yawan jamaa.

To sai dai bisa ga karuwan yawan jamaa musamman a kasar ta masar akwai bukatar a samarda da wata hanya na samun ruwa a wannan yankin,inji kwarraru ta harkokin da suka danganci ruwa.

 • Kwanan wata 22.03.2007
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvSw
 • Kwanan wata 22.03.2007
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvSw