1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bukin nuna finafinan Afirka a Frankfurt

Shirin na mu a wannan karo ya yada zango ne a birnin Frankfurt na nan Jamus inda ake gudanar da bukin finafinan Afirka karon na 15.

default

Finafina sama da 30 daga nahiyar ta Afirka aka gabatar da su a bukin na bana wanda zai kawo ƙarshe a ranar bakwai ga wannan wata na Fabrairu.

Tun ba yau ba kamfanonin shirya finafinai na Hollywood a Amirka suke tafiyar da hulɗa da ƙasashen Afirka inda tare da haɗin guiwar mashahuran ´yan wasan fim na Afirka aka shirya finafinai da suka yi tashe a wajen nahiyar. To amma duk mai son sanin yadda Afirka kanta ke ganin wannan abin zai sha da ƙyar domin ba a nuna waɗannan finafinan gidajen sinima ba yayin da kuma jama´a ba su san masu haɗa finafinan ba.

Wannan dai wani ɓangare ne na wani fim mai suna Divizionz wanda aka haɗa tare da wata ƙungiyar mawaƙa ta wasu matasa huɗu mawaƙan zamani da suka fito daga wata unguwar marasa galihu dake Kampala babban birnin ƙasar Uganda. Burin waɗannan matasan dai shi ne su shahara ko ta halin ƙaƙa. To sai dai saɓanin wasu wuraren, a Afirka zama mashahuri cikin dare ɗaya abu ne mai wahalar gaske saboda matsaloli iri daban daban kama daga ´yan sanda, tsarin zamantakewa da kuma matsanancin talauci. Wanda ya shirya fim ɗin Adi El Assal ɗan ƙasar Masar ya yi bayani game da fim ɗin na Divizionz yana mai cewa.

“Da wannan fim mun yi ƙoƙarin nuna yadda tsarin zaman jama´a ya ke a ƙasar Uganda. Domin a nan za ka iya ganin bambamcin dake akwai tsakanin matalauta da masu hannu da shuni da sauran abubuwan da ba a rasa ba.”

Shi dai wannan Bamasare mai shirya fim na daga cikin tawagar furodusoshin fim na Afirka da ke halartar bukin nuna finafinan na birnin Frankfurt. Ya ce an shirya wannan fim ne akan abokantaka da buri na rayuwa da kuma abin da zai faru idan abokan juna a yau suka zama abokan gabar juna a gobe.

Wannan fim dai na matsayin wani labari irin ainihin abubuwan dake faruwa a rayuwa ta yau da kullum da kuma kaɗe-kaɗe. Saboda haka yana zama wani abin koyi ga masu sha´awar shirya finafinan zamani na Afirka.

“Mun samu kusanta ƙwarai da gaske da ´yan wasan kwaikwayon. Mun haɗa fim ɗin da hannu da kyamarori guda biyu kaɗai, wato ba mu yi amfani da wani kayan aiki na a zo a gani ba. Fim ɗin dai labari ne kawai irin na al´amara amma ba drama ba ne. To sai dai mutane da yawa na da ra´ayin cewa fim ɗin ya yi kyau domin ya ƙunshi sabbin abubuwa da ba a saba gani ba. Tunanin su shi ne mun kashe kuɗi da yawa to amma gaskiya abin da muka kashe bai taka kara ya karya ba.”

Ko shakka babu wannan fim yayi armashi. Duk da cewa ba a kasahe masa kuɗi mai yawa ba, amma kwalliya ta mayar da kuɗin sabulu domin furodusoshin sun yi nasarar yin wani gwaji yadda ´yan Afirka za su iya yin amfani da kuɗi kaɗan don shirya fim. Wannan fim dai ya ɗauki hankali mahalarta bukin na finafinai a Frankfurt inda wasu suka kwantanta shi da finafinan da ake shiryawa a Hollywood. To amma Adi El Assal ba yi jin daɗi idan ana kwantanta aikinsa da na Hollywood. Ya ce ganin yadda fim ɗin Blood Diamond ya yi suna, hakan ba shaida ba ce cewa Hollywood ta gano nahiyar Afirka.

“Me ake nufi da wai Hollywood ta gano Afirka? Dukkan finafinan Hollywood suna cin maƙudan kuɗaɗe kusan dala miliyan 40. Abin da suke yi kawai shi ne suna zuwa da ´yan wasansu Afirka, bayan sun shirya fim sai su yi gaba. Mu kuwa ba ma son haka. Abin da muke so shi ne mu tafiyar da hulɗa ta ƙut da ƙut da mutanen da muke haɗa finafinan a yankunansu, amma ba kawai da an gama sai an manta da su ba. Wato kenan an ci amfani ganga an yar da kwaure.”

Yanzu haka dai an baje kolin finafina fiye da 30 daga Afirka a gidan adana kayan tarihin fim na birnin Frankfurt. To amma finafinai kamar irin waɗanda kamfanin shirya finafinan Nijeriya wato Nollywood ya haɗa ba a nuna su a gun bukin na birnin Frankfurt ba saboda rashin ingancinsu. Wani fim da shi ma ya ɗauki hankali shi ne wanda Katy Lena Ndiaye ta shirya mai taken En attendant les hommes wato cikin jiran mutane a hausa. Fim ɗin akan halin rayuwa ne a garin Walata dake cikin hamadar ƙasar Mauritaniya. A fim ɗin dai an nuna yadda mata a wannan gari suke ba da labarin hulɗarsu da maza.

Natasha Gikas wadda ke ɗaya daga cikin masu shirya bukin nuna finafinan a Frankfurt ta yi bayani kan finafinan Afirka tana mai cewa.

“Ko shakka babu har yanzu ana shirya finafinai game da rayuwar yau da kullum a ƙauyuka na Afirka da kuma fim na tatsuniya, amma fa yanzu an shiga wani zamani na haɗa finafinai na ilimin kimiyya. Alal misali a cikin shekarun baya-bayan nan an haɗa finafinai masu kyau daga Afirka, wanda a da ba zaka taɓa yin tunanin za a iya haɗa su a wannan nahiya ba.”

Ban da waɗannan akwai kuma finafinai da suka shafi siyasa da furodusoshi kamar Haile Gerima da Youssef Chahine da Rachid Bouchareb ko Mahamat Saleh Haroun suka shirya.

Baya ga su akwai sabbin finafinai game da halin da ake ciki a Zimbabwe dake nuna yadda wata yarinya bayan mutuwar mahaifiyarta sakamakon cutar AIDS ta yi ƙaura zuwa Afirka Ta Kudu neman aiki, inda ta samu aiki a matsayin yarinyar gida wadda ake ci da guminta ban da lalatar da mai gidan farar fata yayi ta yi da ita.

Bikin nuna finafinan na Frankfurt ya nuna ainihin finafinan da ke bayyana gaskiyar al´amura a Afirka ba tare da ƙarin gishiri ba, wato ba kamar yadda tashoshin telebijin a nahiyar Turai suke nunawa ba, inda suka fi mayar da hankali wajen wahalhalun da suka yiwa nahiyar ta Afirka katutu, kamar yadda Natasha Gikas ta yi bayani.

“A nan Jamus ana da ƙarancin masaniya game da nahiyar Afirka saboda finafinai ƙalilan ne ake shiryawa a wannan nahiya. Sannan waɗanda aka shirya a can ɗin ma da wuya ake ganinsu a gidajen sinima na Turai. Saboda haka ake yiwa nahiyar wata mummunar fahimta.”

Muhimmin abu ga Natasha Gikas shi ne bukin nuna finafinan na Afirka bai bawa wani fim na Afirka wata ma´ana. Inda an yi haka wato kenan da an sanya finafinai kamar Divizionz, En attendant les hommes da dai sauransu a jerin finafinai na ƙasashe matalauta, abin da masu shirya bukin ke yaƙi da shi.

Sauti da bidiyo akan labarin