1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin Kirismeti a majami´ar St. Peters dake birnin Rom

December 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvF3

Paparoma Benedict na 16 ya yi kira da a karfafa imani, inda a cikin sakonsa na bukin Kirismeti a yau lahadi, ya fadawa masu ziyarar ibada cewa suna fuskantar barazanar kaucewa hanyar Ubangiji idan suka shagala da duniya da kuma ci-gaban fasahohin zamani. Paparoma ya fadawa dubun dubatan mutane da suka hallara a dandalin majami´ar St. Peters dake birnin Rom cewa maza da mata a wannan zamani na ci-gaban fasaha ka iya fuskantar hadarin dake tattare cikin wannan ci-gaba, wanda idan ba su yi hattara ba yana iya gusar da imani daga zuciyar su. A cikin jawabinsa na kirismeti wanda shine na farko a matsayinsa na Paparoma, Benedict na 16 yayi kira da a samar da zaman lafiya a duniya, sannan yayi addu´o´i na musamman don kawo karshen tashe-tashen hankula a yankin GTT da nahiyar Afirka, inda ya ba da misali da rikicin yankin Darfur.