Bukin cika shekaru 65 da ƙarshen yaƙin duniya na biyu | Labarai | DW | 09.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukin cika shekaru 65 da ƙarshen yaƙin duniya na biyu

Dakarun manyan ƙasashen duniya sun yi fareti a wajen shagalin cika shekaru 65 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu

default

Gwamnatin Rasha ta gudanar da shagulgular cika shekaru 65 da yin galaba akan mulkin 'Yan Nazi a Jamus a lokacin yaƙin duniya na biyu, tare da yin faretin dakaru mafi yawa tun bayan rugujewar tarayyar Soviet. Wannan dai shi ne karon farkon da dakarun NATO suka halarci faretin a birnin Moscow, fadar gwamnatin Rasha. Sojoji daga ƙasashen Amirka, Birtaniya da Faransa da kuma Poland, game da na Rasha ne suka yi machi a dandalin Red Square, dake gaban fadar shugaban Rasha ta Kremlin.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, na daga cikin shugabannin da suka halarci bukin, sai dai da dama daga cikin shugabannin Turai sun soke halartar shagalin, domin mayar da hankalin su ga ƙoƙarin kare martabar takardar kuɗi ta Euro daga ƙara faɗuwa a kasuwannin kuɗi na duniya. Shugaba Nikolas Sarkozy na Faransa da kuma Frime Ministan Italiya Silvio Berlusconi, suka ce zasu yi namijin ƙoƙari wajen kare darajar Euro gabannin sake buɗe kasuwannin hada hada gobe Litinin - idan Allah ya kaimu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu