Bukin cika shekaru 27 da juyin juya halin Islama a Iran | Labarai | DW | 11.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukin cika shekaru 27 da juyin juya halin Islama a Iran

Dubun dubatan mutane a Teheran babban birnin Iran sun halarci taron gangamin tunawa da juyin juya halin Islama na shekara ta 1979. Gidan telebiji kasar ya ce yawan wadanda suka halarci taron gangami ya kai miliyoyin mutane. A jawabin da yayiwa taron shugaba Mahmud Ahmedi-Nijad ya sake yin suka ga kasashen yamma da kuma Isra´ila. A dangane da takaddamar da ake yi akan shirin nukiliyar Iran kuwa shugaba Ahmedi Nijad yayi barazanar janyewa daga yarjejeniyar da ta hana yaduwar makaman nukiliya a duniya. Shugaban ya ce kawo yanzu kasar na aiki a karkashin wannan yarjejeniya kana kuma ta biyayya ga dokokin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.