Bukin al´adun Afrika a Würzburg | Zamantakewa | DW | 21.06.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bukin al´adun Afrika a Würzburg

Bukin al´adu da waƙoƙin Afirka a Würzburg shi ne mafi girma a Turai

default

Mawaƙi a Bukin Würzburg

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, wanda a ciki muke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi daban daban na wannan duniya ta mu.

A shirin na yau za mu yada zango ne a birnin Würzburg na nan Jamus inda kamar a kowace shekara a bana ma aka gudanar da bukin ƙasashen Afirka wanda ke zama irinsa mafi girma a nahiyar Turai.

A bukin al´adun Afirka na wannan shekara a birnin Würzburg an gayyaci dukkan fitattun makiɗa da mawaƙa daga nahiyar mu ta Afirka, ciki har da Yousouf N´Dour daga Senegal da Manu Dibango daga Kamaru. Bukin na kwanaki huɗu ya samu halarcin mutane fiye da dubu 100, waɗanda suka shaida wani ƙasaitaccen shagalin cika shekaru 20 da fara wannan buki a Würzburg.

Taken fara gudanar da wannan buki shekaru 20 da suka wuce na matsayin wata tsokana wato waƙoƙi a matsayin taimakon raya ƙasar Jamus. Wani ƙaramin bukin da aka fara a wata unguwa dake birnin Würzburg a shekarar 1989 yanzu ya zama wani bukin waƙoƙi da al´adun Afirka mafi girma a nahiyar Turai. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier shi ya buɗe bukin na bana.

Steinmeier:

Ya ce „Ina maraba da dukkan mutanen da suka hallara a wannan buki. Masu iya magana kann ce hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. Yau dai kun shaida irin ci gaban da muka samu bayan mun haɗa hannu wuri guda.“

Burin da aka sa a gaba shi ne mayar da wannan bukin ya zama matattarar makiɗa da mawaƙa na duniya baki ɗaya hare da wakila daga fannin siyasa da na tattalin arziki waɗanda ke mayar da hankali kan abubuwan masu alfanu dake faruwa a nahiyar Afirka.

Shugaban bukin na al´adun Afirka a birnin Würzburg karo na 20 shi ne shahararren mawaƙin nan na Kamaru wato Manu Dibango wanda ya yi suna a kiɗansa na Soul Makossa da ya haɗa salon waƙoƙin Jazz, Soul, Reggae da dai sauransu.

Dibango

Ya ce “Wannan buki yana ba da gudunmawa wajen inganta dangantaku tsakanin Turai da Afirka. Mutane da yawa na nuna sha´awarsu ga nahiyar Afirka musamman dangane da albarkatun ƙarƙashin ƙasa da Allah Ya huwace mata wato kamar man fetir, iskar gas da lu´ulu´u. Amma kaɗan ne ke sha´awar salon rayuwar al´ummomin Afirka. To amma bukin na Würzburg ya na mayar da hankali kan al´adun Afirka wadda mu masu fasahar kiɗa da waƙoƙin wannan nahiya muke wakiltar al´ummominta. Yau dai shekaru ɗai-ɗai har 20 kenan Jamus tana nuna sha´awarta ga nahiyar Afirka ta hanyar gudanar da wannan gagarumin buki. Na sha halartar wannan buki kuma na yi ta saduwa da takwarorina mawaƙa waɗanda da wataƙila ba zan taɓa haɗuwa da su a Afirka ba. Lalle dole ka zo birnin Würzburg don ganewa idonka abubuwa masu ban al´ajabi.”

Manu Dibango wanda ke magana cikin raha da annashuwa, kamar yadda aka saba bai ajiye baƙin tubaraunsa ba a kiɗan buɗe bukin na waƙoƙin Afirka Würzburg. Da shi da wani sanannen makaɗin waƙoƙin jazz na nan Jamus wanda kuma shine baƙo na musamman a bukin wato Klaus Doldinger mai shekaru 72 suka haɗa wannan kiɗa. Klaus da takwaransa na Afirka wanda yanzu ya cika shekaru 74 da haihuwa sun nunawa mahalarta bukin cewa da tsohon zuma ake magani.

Manu Dibango da Klaus Doldinger ba su taɓa haɗuwa ba sai a wurin bukin na Würzburg. To amma sun naƙalci waƙoƙin juna ta yadda ba su yi wani gwaji na dogon lookaci ba kafin su rera wannan waƙa da suka yi a gaban dubun dubatan ´yan kallo.

Doldinger

Ya ce “Wannan dai wani abin ban sha´awa ne ga waƙa inda ba zato ba tsammani sai kai da wani ku rera waƙa. Ban da wani bayani dangane da haka. Na san waƙoƙin Manu Dibango. Na yi maraba da shawarar ta rera waƙa tare da shi. Amma ban taɓa tunanin hakan zai yiwu ba, domin ban san cewa yana da ƙwararrun makiɗa haka ba.”

Babban burin bukin na Afirka a birnin Würzburg shi ne amfani da waƙa a matsayin wata haɗaka tsakanin nahiyoyi daban daban tare da nunawa duniya ɗinbim arzikin al´adu da al´ummomin daban daban da Allah Ya bawa a nahiyar Afirka da zumar ƙarfafa tuntuɓar juna tsakanin al´adu daban daban. Haka dai ya ƙara fitowa fili ta hanyar girke-girke da kayakin fasaha da al´adu da aka baje kolinsu a gun bukin. Ga dai ra´aoyin wasu mahalarta wannan buki.

“Tun a ranar Alhamis muke nan wurin. Muna morewa ne kawai musamman yadda mutane daban daban daga ko-ina cikin duniya suka haɗu. Muna jin daɗin waƙoƙin da kayakin da aka baje kolinsu a rumfunan.”

“Ina ganin yanzu wannan bukin Afirka shi ne mafi girma a Turai. Yana da ban sha´awa kuma ya zama na ƙasa da ƙasa. Da zan fi son ganin ´yan Afirka da yawa a nan.”

“Muna zuwa nan a kowace shekara. Ina sha´awar bukin al´adu da launuka daban daban da kuma baje kolin kayakin al´adun gargajiya na Afirka.”

Masu sha´awar kayakin fasahar na Afirka haƙansu ya cimma ruwa a rumfar Mamadou daga Mali, wanda a kowace shekara taƙanas ta Kano ya ke tasowa daga birnin Bamako zuwa birnin na Würzburg don sayar kayakin gargajiya musamman na wasan yara. Haɗuwar makiɗan Afirka da takwarorinsu na duniya na matsayin wani abin sha´awa ga bukin na Würzburg, wanda a bana ma ya samu halarcin mashahurin mawaƙin nan na ƙasar Senegal Yousouf N´Dour, wanda ya shaida gagarumin ci-gaban da aka samu musamman ga maziyarta wannan buki.

N´Dour

“Yanzu dai mahalarta bukin na Würzburg sun naƙalci waƙoƙin Afirka. Dukkansu suna cashewa ba kamar yadda ya kasance shekaru 15 baya ba. A wancan lokacin suna zuwa gani da ido ne amma ba su fahimci salon waƙoƙin Afirka ba. Yanzu da bukin ya cika shekaru 20 mutane sun san ƙabli da ba´adi na waƙoƙinmu. Hakan ya ba ni sha´awa musamman ganin yadda suke maraba da waƙoƙinmu na gargajiya da na zamani.”

Wani rahoto da mujallar Times ta buga yayi nuni da cewa N´Dour na daga cikin mutane 100 mafiya angizo waɗanda suka canza yanayin zamantakewa a duniya. N´Dour wanda wata majullar Birtaniya ta bayyana shi da cewa shahararren mawaƙin Afirka na ƙarni yana kafa wata gidauniya mai suna Birima wadda ke ba da basussuka ga masu ƙaramin ƙarfi a Afirka.

N´Dour

“Wannan dai wata ƙaramar gudunmawa ce da na ke bayarwa wajen yaƙi da talauci. Yanzu mutanen Afirka suna son yin aiki amma da yawa daga cikinsu ba sa samun rance daga bankuna domin har yanzu ana bin tsohon tsarin aikin bankuna ne a Afirka. Mutane ba sa iya cike ƙa´idojin ba da rance na bankuna. Saboda haka gidauniyar Birima ta na ba da taimakon kuɗin don yin wasu aikace aikace ba tare da gindaya wasu sharuɗɗa ba. Na yi imani wannan ita ce hanya mafi dacewa wajen yaƙi da talauci.”

Yousouf N´Dour na mai ra´ayin cewa ƙananan basussuka da koma ga bin al´adun gargajiya su ne mabuɗin samun ci-gaban nahiyar Afirka. Raya wannan al´ada ta gargajiyar ce kuwa ya sa ake ɗokin halartar bukin na Würzburg.