Bukatar zaman lafiya a kasar Congo | Labarai | DW | 02.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar zaman lafiya a kasar Congo

Hukumar tarayyar turai ta yi kiran yin taka tsantsan da kuma kwantar da hankula a yayin da ake jiran sakamakon zaben da aka gudanar a kasar Congo karo na farko bisa tsarin jamíyu da dama a tsawon shekaru 46 a tarihin kasar.kwamishiniyar danganta da kasashen waje na kungiyar tarayyar turai Benita Ferrero Waldner ta yi kira alúmar kasar Congo da dukkan magoya bayan yan takara su nuna hakuri da juriya a yayin da ake dakon sakamakon zaben. Ta yi kira ga dukkan jamiyu da yan takara su gabatar da koken su ga hukuma idan suna da wani korafi a game da zaben. Shi ma Kwamitin kasa da kasa mai tallafawa dimokradiya a Jamhuriyar dimokradiyar Congon ya yi kashedi ga yan siyasa da kafofin yada labarai da su guji baza jita jita a sakamakon kuriún da ake kidayawa. Kwamitin yace irin wannan soki burutsu na haifar da rudani a tsakanin alúma wanda kuma ka iya kaiwa ga tada zaune tsaye. Zaben shugaban kasa dana yan majalisun dokoki da aka gudanar a kasar sune farko daga cikin zabukan da aka shirya a kasar wanda ake fatan kammalawa ya zuwa karshen wannan shekarar.