Bukatar Sojan kiyaye Zaman Lafiya Daga Jamus | Siyasa | DW | 02.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukatar Sojan kiyaye Zaman Lafiya Daga Jamus

Majalisar dinkin Duniya na bukatar ganin Jamus ta ci gaba da ba da karin gudummawar sojojinta domin ayyukan kiyaye zaman lafiya, musamman ma a kasar kongo inda al'amura ke dada yin tsamari

A cikin wani jawabin da yayi ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya fito fili ya bayyana matsayin Jamus a siyasar duniya inda yake cewar:

Tilas ne mu rungumi alhakin da ya rataya a wuyanmu dangane da ire-iren ci gaban da ake samu a siyasar duniya. Jamus ba zata yi sako-sako da matakan tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiyar duniyar ba.

Wannan bayanin na Joschka Fischer na ma’ana ne cewar Jamus ba zata iya kin ba da gudummawa gwargwadon ikonta a ayyukan kiyaye zaman lafiya ba, ko da kuwa kasar ba ta samu wakilci na dindindin a kwamitin sulhu na MDD ba. Ana bukatar sojan kasar a can gabacin Afurka da Kosovo da Afghanistan, kuma mai yiwuwa a kasashe kamarsu Sudan ko Kongo nan gaba kadan. Al’amura sun canza suka dauki wani sabon salo a game da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD in ji Gunter Pleuger, jakadan Jamus a majalisar. A halin yanzu haka majalisar na da sojojinta dake aikin kiyaye zaman lafiya kama daga Kongo da Haiti zuwa Saliyo da Cyprus da Lebanon da yammacin Sahara da dai sauran yankunan da ake fama da rikice-rikice a cikinsu. Shi kansa sakatare-janar Kofi Annan ya kan shiga rudu da rashin sanin tabbas sakamakon gibin sojojin da MDDr ke fama da shi. Ko shakka babu bukatar sojojin zata dada karuwar ganin yadda al’amura ke ci gaba da yin tsamari a sassa dabam-dabam na duniya ita kuma MDDr bata kaunar ganin an sake fuskantar wata ta’asa ta kisan kare-dangi irin shigen wacce aka fuskanta a kasar Ruwanda shekaru goma da suka wuce. A lokacin da ya ke bayani, sakatare-janar Kofi Annan cewa yayi:

Wajibi ne kowace kasa, kome girma ko kankantarta, ta ankara da gaskiyar cewar zaman lafiya da kwanciyar hankalinta ya ta’allaka ne da zaman lafiyar duniyar baki daya.

Ita dai MDD bata da wata tsayayyar runduna ta mayaka, ta dogara ne akan karo-karon sojoji na kasashenta domin tafiyar da ayyukanta na kiyaye zaman lafiya, kuma yawa-yawanci jakadun kasashenta ne ke gabatar da rokon gudumawar sojojin ga gwamnatocinsu a wawware.