Bukatar sauya salo a yaki da IS | Siyasa | DW | 21.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukatar sauya salo a yaki da IS

Turai na nazarin matakan da suka fi dacewa kan wannan kungiya ta 'yan ta'adda, ganin cewar ya zuwa yanzu, nasarorin da suke samu kan kungiyar ba su taka kara sun karya ba

Akwai alamun cewar kasashen yamma sun kai ga fahimtar cewar jefawa mayakan kungiyar IS bama-bamai kawai ba zai sanya su sami nasarar kawar da kungiyar kamar yadda suke so ba. Saboda haka ne ake iya tambayar: Shin hanyoyin da kasashen na yamma suke bi na yaki da IS su ne suka fi dacewa? Richard Atwood, na cibiyar nazarin rikice-rikice ta kasa da kasa, wato International Crisis Group, ya ce:

Kungiyar IS tana cin gajiyar yake-yake dake tashi a yankuna dabam dabam da kuma rushewar kasashe da ake samu.

Cibiyar dai a kwanan nan ne ta gabatar da wani rahoto kan yadda kungiyar IS take kara karfi a aiyukanta. Masanan suka ce tuni an san cewar yake-yake na basasa da rashin kwanciyar hankali a kasashe kamar Irak ko Siriya, sune manyan al'amuran dake taimakawa kungiyoyin yan ta'adda, kamar yadda ake gani yanzu game da al-Qaeda a Afghanistan. A game da IS kuwa, kungiyar tana sane da cewar abokan gabanta da kansu zasu tashi su rika yaki da junansu.

Atwood yace idan mutum ya duba gaba dake tsakanin Saudi Arabiya da Iran, muna iya gane cewar nasarorin da IS take samu da kuma yadda kungiyar Al Qaeda take kara karfi, duka suna samuwa ne daga kura-kuran abokan gaban wadannan kungiyoyi, amma ba daga karfin da su kansu suke dashi ba.

Kasashen Turai suna da ra'ayin cewar tun da an sami nasarar kawo manyan abokan gaba biyu, Iran da Saudi Arabiya kan teburin shawarwari tare da kasashen Rasha da Amirka da Kungiyar Hadin Kan Turai, idan har aka sami nasarar sassauta yakin dake tsakanin shugaban Siriya, Bashar al-Assad da abokan adawarsa, ana iya maida hankali kan yadda ya fi dace a yi yaki da IS. Richard Atwood saboda haka ya ce:

A tattaunawar da za a yi, bai kamata a maida hankali kan ko ya kamata Bashar al-Assad ya janye daga mulki, ko ya ci gaba kan kujerarsa ba.

A ra'yinsa, abin dake da muhimmanci shine yan darikar Sunni wadanda daga garesu ne kungiar IS ta bullo, a samar masu da makoma mai haske a kasashen Iraki da Siriya, saboda kamar yadda ya ce:

Kungiyar IS ta samu ne daga taimakon dukkanin bangarorin siyasa a kasashen biyu, kuma musamman a a Irak kungiyar ta bullo ne saboda yadda aka maida mabiya darikar Sunni a kasar saniyar ware.

Daya daga cikin manufofin da Kungiyar Hadin Kan Turai ta tsara a gabas ta tsakiya shi ne: bayan an kwato da yankunan Siriya da Iraki daga aiyukan kungiyar ta IS, kada a kyale a rika daukar fansa kan yan Sunni a kasashen biyu. Da alamun cewar ko da shike kasashen na Turai a shirye-suke, su dauki darasi daga kura-kuran da suka yi a can baya kan yaki da IS, abin da ba'a sani ba shine ko sabbin manufofin da suka bullo da su na yaki da tarzoma za su kai ga biyan bukata.

Masu binciken na cibiyar nazarin rikice-rikice ta kasa da kasa sun kuma nunar da cewar kawar da kungiyar IS daga wuraren da suka kakkafa khalifofinsu kawai ba zai wadatar ba. Idan har suna son raunana wannan kungiya tilas su maida hankali ga masu goyon baya da rufawa IS baya, wato matasan kasashen na Turai.