1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar sanya wa'adin kawo karshen rikicin Siriya

March 31, 2012

Hadin gwiwar Amirka da kasashen yankin tekun Fasha sun bukaci Kofi Annan ya sanya wa'adin lokaci ga shugaba Assad ya kawo karshen zubar da jini a Siriya.

https://p.dw.com/p/14VvA
A handout picture made available by the Saudi Press Agency (SPA) shows Saudi King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud (L) next to Prince Salman bin Abdul Aziz Al Saud (R) before leaving for treatment to the US, in Riyadh, Saudi Arabia, 22 November 2010. King Abdullah of Saudi Arabia was to travel to the United States for medical treatment, according to well- informed sources in Riyadh. The King has mandated his half brother, Crown Prince Sultan bin Abdulaziz to 'administer the nation's affairs' in his absence. The Crown Prince was due to arrive in Riyadh before Abdullah's departure. EPA/SAUDI PRESS AGENCY - HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Amirka da kasashen yankin tekun fasha sun yi kira ga wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya da kasashen larabawa kan rikicin Siriya Kofi Annan ya sanya wa'adin lokaci da zai umarci shugaban Siriya Bashar al-Assad ya aiwatar da shirin zaman lafiaar da aka gabatar domin kawo karshen cin zarafin da ake yiwa masu bore. Hadin gwiwar Amirka da Ministocin harkokin waje na kasashen yankin tekun fasha a cikin wata sanarwa ta suka fitar a karshen taron da suka gudanar yau a birnin Riyadh na kasar Saudiyya sun bukaci Kofi Annan ya zayyana matakin da ya kamata a dauka idan gwamnatin Assad ta ci gaba da hallaka al'umarta.

Sanarwar bayan taron na hadin gwiwa ya kuma bukaci kasashe wadanda ke da alaka ta kai tsaye da gwamnatin Siriya su bi sahun gamaiyar kasa da kasa a yunkurin kawo karshen rikicin na Siriya. Da ta ke tsokaci sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta yi bayani da cewa " Gwamnatin Siriya abin takaici ta nuna halinta ina ta ke daukar alkawura amma kuma ta ki cikawa, saboda haka a yau ni da takwarori na Ministoci mun amince kan bukatar dakatar da kashe kashen rayukan jama'a nan take mun kuma bukaci manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya da kasashen larabawa ya sanya wa'adin lokaci na mataki na gaba". Gwamnatin Siriyar dai ta ce ta kawo karshen boren da aka shirya domin kifar da mulkin shugaba Bashar al-Assad.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman