Bukatar koyar da darasin addinin Islama a makarantun Jamus | Labarai | DW | 14.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar koyar da darasin addinin Islama a makarantun Jamus

Wata sabuwar hadaddiyar kungiyar musulmi dake nan jamus ta nemi gwamnatin kasar data basu yanci daidai dana sauran addinai dake nan kasar,tare da tabbatar dacewa ana koyarda ilimin addinin musulunci a dukkan makarantu dake fadin kasa.Sakatare general na kasa na kungiyar musulmin Aiman Mazyek,ya bayyana cewa makasudun yin hakan shine cikanta hanyoyin rayuwa na bai daya,wanda kuma zai gabatar a taron da zasu gudanar da ministan harkokin cikin gida Wolfgang Schaeuble afarkon watan mayu.

Ya bayyana cewa laakari da yancin musulunci,zai bada dama wa dukkan makarantu dake nan kasar ,na koyar da shi.