Bukatar karfafa tsaro a jihar Filato
October 17, 2017Wannan kira da al'ummar ta yi dai na kunshe ne cikin wani taron manema labarai da ta kira bayan harin da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 30 a ranakun Lahadi da Litinin, inda shugaban kungiyar raya ci gaba al'ummar ta Irigwe ta kasa bakidaya Sunday Abdu, ya ce a tsakanin mako guda an kashe mutane fiye da 40 akasarin mata da yara da kuma tsoffi.
Suma a nasu bangaren shugabanin kungiyar Miyyetti Allah ta jihar Filato, sun yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa mazauna kauyukan karamar Bassa kuma sun ensanta kansu daga harin.
To sai dai kuma wasu na zargin sakaci daga bangaren gwamnatin jihar wajen daukan matakan dakile rikicin, zargin da mashawarcin gwamnan Filato kan ayyukan watsa labarai Dang Jang, yace ba'ayi wa gwamnatin adalci ba.
Masharhanta dai sun lura yakamata gwamnatin jiha ta tashi haikkan wajen magance lamarin wannan matsala ta hare-hare, tun kafin abin ya zarce hankali. Tun ranar Litinin gwamnatin jihar Filato ta ayyana dokar hana zirga-zirga a karamar hukumar Bassa daga karfe shida na yamma zuwa karsfe shida na safe.