Buhari zai gana da Trump
April 16, 2018Fadar White House ta Amirka, ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki a kasar inda zai gana da takwaransa Donald Trump a birnin Washington. A cewar wata sanarwar da ta fitar, fadar ta White House ta ce ganawar shugabannin biyu, wadda za a yi ranar 30 ga wannan watan na Afrilu, za ta tabo batutuwan tattalin arziki da yaki da ta'addanci. Akwai ma batun kyautata tafiyar Najeriya a demokuradiyyance, saboda tasirin kasar a siyasar nahiyar Afirka.
A makon jiya ne dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana aniyar sake tsayawa takara a zaben da za a yi a badi, abin kuma da ya sanya wasu ke kiraye-kiraye da kar ya yi hakan. Kasar ta Buhari dai na fuskantar matsalolin tsaro ta fuskoki da dama, duk da damarar da gwamnatinsa ta ja na sama wa lamarin magani.