Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kudi | Labarai | DW | 06.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kudi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudi na wannan shekara ta 2016 bayan da ya yi tamar da shi majalisa don gyara.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudi na wannan shekara ta 2016 da muke ciki, wanda ya kawo karshen dogon dako ko kuma jiran tsammani daga al'ummar kasar.

Wani shaidan gani da ido daga kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya bayyana cewa Buhari ya sanya hannu ne kan kasafin kudin bayan kawo karshen kiki-kaka din da aka yi ta samu tsakanin majalisar dokokin kasar da kuma bangaren zartaswa.

Rahotanni sun nunar da cewa daga cikin kudirin da gwamnati ta yi na yin amfani da kasafin kudin na bana da yawansa ya kai sama da dalar Amirka biliyan 30 dai, har da kawo karshen matsin tattalin arzikin da talakawan Tarayyar Najeriyar suke fama da shi a sakamakon faduwar farashin gangar danyan mai a kasuwannin duniya.