Buhari ya nemi karin hutu don duba lafiyarsa | Siyasa | DW | 05.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari ya nemi karin hutu don duba lafiyarsa

A cikin wata takarda da aike wa majalisar dokokin Najeriya shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar ta kara masa lokacin hutu domin duba lafiyarsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dokokin kasar ta kara masa hutu domin duba lafiyarsa a cewar wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasar. 

Sanarwar ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya aike da takarda ga majalisar dokoki a yau Lahadi 5 ga watan Fabrairu 2017 yana sanar da bukatar tsawaita hutunsa domin kammala wasu gwaje gwajen lafiya da likitoci suka bada shawarar a yi masa.

Tun farko shugaban ya dauki hutun makonni biyu domin duba lafiyarsa a Birtaniya.

Karin lokacin da shugaba Buharin ya nema dai ka iya yin tasiri akan amannar da ake da ita akan gwamnatinsa a daidai lokacin da ta ke fuskantar suka kan tsadar rayuwa da kuma yadda gwamnatin ke tafiyar da lamuranta.

Shugaban ya shirya komawa gida ne a yammacin yau to amma likitoci suka bashi shawarar jinkirtawa domin kammala gwaje gwajen lafiyar.