1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya gana da 'yar makarantar Chibok

Ubale Musa/ MNAMay 19, 2016

Cikin murna Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da daya a cikin sama da 'yan mata 200 da Boko Haram ta sace shekaru biyun da suka gabata a Chibok.

https://p.dw.com/p/1Iqqu
Nigeria Befreiung des ersten Chibok-Mädchens
Gwagwarmaya har sai an gano sauran 'yan matan da ke hannun Boko HaramHoto: DW/K. Gänsler

A cikin wani yanayi na farin ciki da tsallen murna ne dai shugaban Tarrayar Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi daya a cikin sama da 'yan mata 200 da kungiyar Boko Haram ta kai ga sacewa shekaru biyun da suka gabata daga makarantarsu da ke garin Chibok na jihar Bornon Najeriya.

Da ranar Laraba dai aka sanar da tsintar Amina Ali da mijinta da 'yarta daya a cikin dajin Sambisa a wani abun da ke zaman ba zata da kuma ya dauki hankali ciki da ma wajen Najeriya. Tun a watan Afrilun shekara ta 2014 ne dai 'yan kungiyar Boko Haram suka kame 'yan mata sama da 276 a makaranatar sakandaren garin na Chibok.

Nigeria Eine der durch Boko Haram verschleppten Schülerinnen ist frei
Daya daga cikin 'yan matan Chibok da aka ceto ana duba lafiyartaHoto: picture-alliance/dpa/Nigerian Military

Gwagwarmayar ceto 'yan matan dai ta dauki hankali ciki da ma wajen kasar abun kuma da ya kai ga haihuwar kungiyar "Bringback our Girls" da ta jajirce ga bukatar neman 'yan matan.

Fatan cigaba da jan aikin neman sauran 'yan mata

Duk da cewar dai ana ta'allaka samo daya a cikin 'yan matan da wasu 'yan kungiyar sa kai dai, ranar na zaman ta farin ciki da ban hakuri ga gwamnatin kasar a fadar ministan tsaron kasar Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, wanda ya kara da cewa "da ma mun ce su yi hakuri kuma sannu a hankali za a gano sauran 'yan matan."

Nigeria Befreiung des ersten Chibok-Mädchens
Cigaba da addu'a har sai an gano sauran 'yan matanHoto: DW/K. Gänsler

Shi ma daida gwamnan jihar Borno Kasim Shatima da ya jagoranci dauko uwar da ma jaririyar ya zuwa fadar shugaban kasar ya ce yana da kwarin gwiwar samo yaran a cikin lokaci na kankane a nan gaba in har sojan kasar sun cigaba da irin jan aikin da suke yi yanzu. Ya ce da yardar Allah za a kai ga ceto 'yan matan.

Ko bayan gwamnatin kasar da ta dauki alhakin ilimi da ma kula da rayuwar ta Amina Ali dai ita kungiyar "Bringback our Girls" mai fafutukar neman 'yan matan dai ta ce gano Aminar na zaman sabon fata ga tabbatar da kai makomar 'yan matan a fadar Hadiza Bala Usman daya daga cikin jagorori na kungiyar.

Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba a kokarin gano ragowar 'yan matan da har yanzu ake jin sun yi nisa a cikin dajin na Sambisa.