1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari ya fasa zuwa duba lafiyarsa a Ingila

Shugaban tarrayar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya soke komawa birnin London domin ci gaba da magani kamar yadda ya tsara, sakamakon rikici tsakanin gwamnatinsa da 'yan majalisar dattawa..

Jim kadan da saukarsa a tarrayar najeriya daga wani hutun magani na watanni biyu, shugaba Muhammadu Buhari bai boye burinsa ba na sake komawa domin ci gaba a cikin duba lafiyarsa. sai dai babu zato kuma ba tsammani, shugaban kasar ya ce ya fasa kuma a maimakon hakan zai gayyato likitocin na Ingila domin dubashi a Abuja. Duk da cewar har yanzu babu sanarwa daga fadar gwamnatin kasar da ke tabbatar da haka, tuni  dai labarin soke tafiyar ta shugaban ya mamaye kafafen yada labarai na Najeriysa tare kuma da jawo muhawara cikin kasa.

Soke ziyarar a daidai lokacin da lamura ke sukurkucewa a cikin fadar shugaban kasa na kara nuna alamun bukata ta shugaban na kyakyawan nazari domin tinkarar Karin rigingimu a ciki da wajen fadar. Abun kuma da  a cewar  Dr Garba Umar Kari da ke nazari a cikin harkokin kasar, ke zaman abun da ya dace a cikin yanayin da gwamnatin kasar ke fuskanta yanzu.

Ana dai ci gaba da rikicin a tsakanin jiga-jigan mazauna fadar shugaban kasa dama bangaren zartarwa da na majalisa,  a wani abun da ke barazana ga harkokin gwamnatin 'yar sauyi. Sai dai a tunanin Malam Yusuf Din Gyadi da ke zaman jigo ga adawa, babbar matsalar Najeriya na zaman alamun gazawa ta Buharin da ke zaman maigidan dake neman kare harkokin cikin gidansa.

 

Sauti da bidiyo akan labarin