Buhari: Sauya kasafin kudi bai mana dadi ba
June 20, 2018Talla
Shugaban na Najeriya ya ambata hakan ne dazu bayan da ya sanya hannu kan kasafin kudin da majalisa ta amince da shi. Tun bayan hawansa mulki, an yi ta samun tinja-tinja tsakaninsa da 'yan majalisar a kan kasafin kudi da kuma wasu kudirorin na ciyar da kasar gaba daidai lokacin da al'ummar kasar ke bayyana damuwar su game da irin jan kafar da ake samu daga bangarorin biyu a kan ayyukan raya kasa.