Buhari: Shekara guda kan mulki da sauran aiki | Siyasa | DW | 27.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari: Shekara guda kan mulki da sauran aiki

Daf da lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi shekara daya a kan mulki kasar na tattare da matsaloli na tattalin arziki da na Boko Haram da kuma rigingimu tsakanin manoma da makiyaya da dai sauransu.

Yayin da gwamnatin jam'iyyar APC karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta cika shekara guda da fara aiki a Najeriya al'ummar kasar sun amince da cewar an samu nasara a fannin tabbatar da tsaro.Kafin zabukan shekara ta 2015 al'amuran tsaro sun tabarbare ta yadda bangarorin kasar a yankin Arewa maso gabashin Najeriya suka koma karkashin abin da mayakan Boko haram suka ayyana da sunan Daular musulunci.Haka kuma a yankin dole jama'a suka yi wa kansu kiyamun laili a kasuwanni da tashoshin mota gami da wuraren taruwar jama'a wajen fitowa don kare kawunansu saboda tsanantar hare-haren kunar bakin wake.

Nasara dakile Boko haram da gwamnatin Buhari ta yi

Bayan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbi jagorancin kasar ta yi wasu sauye sauye tare da maida cibiyar ba da umurni tsaron Najeriya zuwa Maiduguri abin da ake ganin ya haifar da gaggarumar nasara wajen tabbatar da tsaro a kasar.Haka kuma an samu saukin rigingimi da ake alakantawa da kabilanci wanda a baya suka zama babbar matsala musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Karuwar wasu matsaloli bayan na Boko Haram a Najeriyar

Sai dai yayin da ake kashe wata wutar wata kuma na kunnuwa don kuwa an samu karuwar matsalar sace mutane tare da yin garkuwa da su wajen neman kudi da kuma karuwar rikicin tsakanin makiyaya da manoma, da kuma wanda ake alakantawa da hare-haren ramuwar gayya da ake zargin makiyaya na kai wa wasu yankunan kasar.Haka kuma sake dawowar hare-haren tsagerun Niger Delta da kuma zargin kisan kiyashin da sojojin Najeriya suka yi ‘yan Shi'a a Zaria na neman dakushe irin nasarorin da gwamnatin ta cimma a fannin tsaro.

Sauti da bidiyo akan labarin