Buhari ba zai halarci taron kolin AU ba
March 19, 2018Soke halartar taron da ake soma yi a kasar Ruwanda da shugaban Buhari ya yi, ya ja hankulan jama'a musanman masu masana'antu da 'yan kasuwa kan illar janyewa daga taron da ake ganin zai yi matukar tasiri a kokarin da ake na bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Duk da cewar an kira damar karin tattaunawa da Buhari ya bukaci ya yi da kungiyoyin kwadago a matsayin babbar hujjar janyewar Najeriya daga rattaba hannu a bisa yarjejeniyar ciniki na bai daya a kasashen nahiyar Afirka.
Najeriya za ta aika da tawaga zuwa taron na birnin Kigali, janyewar Najeriya da ake yi wa kallon jigo ga kokari na gamayya a tsakanin kasashen Afirkan dai na zaman gagarumin koma baya a cikin yarjejeniyar. Kungiyar kasashen AU na kallon yarjejeniyar a matsayin damar habakka ciniki a tsakanin juna.
Tuni kungiyar kwadago Najeriya ta NLC ta gargadi mahukuntan na Abuja da kada su kuskura su rattaba hannu a bisa yarjejeniyar da a cewarsu ke zaman mai hatsari ga makomar kasar. Ko bayan batun makamashi, babbar matsala ga kasuwar Najeriya a halin yanzu na zaman kwararar kayayyakin waje kama daga shinkafa ya zuwa nama har da man girki da ko bayan barazana ga lafiya ke kuma karya farashi ga kayayyakin gidan da farashin ke neman tashi.