Bude zaman majalisar ECOWAS a Abuja,Nigeria. | Labarai | DW | 13.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bude zaman majalisar ECOWAS a Abuja,Nigeria.

Yau ne aka bude taron majalisar dokoki ta biyu na kasashen dake kungiyar ciniki ta yammacin Afrika watau ECOWAS a birnin Abujan Nigeria.Kimanin wakilan majalisar dokoki 115 daga kasashe 14 daga cikin 15 dake wannan kungiya ce,ke halartan.Dayake bude zaman taron sakaren gudanarwa na ECOWAs Mohammad Ibn Chambers yace kasar Ivory Coast ce kadai bata aike da sunayen yan majalisa da zasu wakilce ta ba,wanda ya kasance kamar a majalisar wakilan na farko.Duk dacewa babu bayanai a hukumance dangane da rashin tura wakilanta Abujan,majiya daga Ivory Coast din na nuni dacewa bata ji dadi da adadin wakilai da aka gabatar mata bane.Shugaban majalisar Dottawan Nigeria Ken Nnamani ,yace tarayyar majalisar zata taimaka wajen cigaban tattali da harkokin rayuwa da siyasa na alummomin yankin yammacin Afrika.Majalisar dake zama na biyun irinsa dai,namai kasancewa daya daga cikin muhimman ressan kungiyar ta ECOWAs mai waadin shekaru 4.