1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude taron shugabannin kasashen Afurka

Ahmad Tijani LawalJanuary 31, 2008

Shugabannin Afurka sun fara taron su a cibiyar kungiyar AU dake Kasar Habasha

https://p.dw.com/p/D0d1
Alpha Oumar KonareHoto: picture-alliance/ dpa

A yau alhamis dinan ne shuagabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Afurka suka bude taron kolinsu na yini uku a birnin Addis Ababa a karkashin taken:"Ci gaban masana'antu a Afurka" to sai dai kuma kamar yadda aka saba a zamanin baya, a wannan karon ma da wuya shuagabannin su samu wata kafa ta dukufa akan wannan batu ta la'akari da rikice-rikicen dake addabar nahiyar Afurka, kama daga Somaliya zuwa Darfur da kuma kasar Kenya a baya-bayan nan.
An gabatar da taron kolin na kungiyar tarayyar Afurka ne tare da zabar shugaba Jakaya Kikwete na kasar tanzaniya a matsayin sabon shugaban kungiyar. Domin mayewa gurbin shugaba John Koufor na kasar Ghana. A cikin jawabinsa na amincewa da zabensa da aka yi shugaba Kikwete ya ce sau tari mu kan ji kunya a game da labaran rikice-rikice a nahiyar Afurka da muke samu a kodayaushe. Wajibi ne da farkon fari Afurka ta dogara da kanta a maimakon kasashen ketare, duk da cewar kawayen nahiyar a shirye suke su taimaka mata. Kuma ko da yake maganar raya makomar masana'antu a nahiyar Afurka ita ce taken taron kolin na shuagabannin kungiyar AU, amma abin da ya fi daukar hankali shi ne rikice-rikicen Darfur da Somaliya da kuma Kenya. An ji daga bakin wakiliyar Amurka akan al'amuran Afurka Jendayi Frazer tana mai nanata zargin matakan tsaftace kabila da ake dauka a kasar Kenya:
"Jendayi Frazer ta ce: ina nanata maganar da tayi tun farko na cewar ana daukar matakan tsaftace kabila a kasar Kenya. Na yi hira da mutane da dama da kaddara ta rutsa da su a Eldoret, wadanda suka ba ni labari cewar gung-gungun 'yan ta-kife ne suka fatattake su, suka kuma tilasta musu da su tattara nasu ya nasu su san inda dare yayi musu. Duk wanda ya nuna taurin kai sai a kai masa hari ko ma a kashe shi baki daya. Hakan na ma'ana ne cewar akwai wasu kabilun dake bakin kokarinsu wajen ganin wasu kabilun sun bar yankuna na kasar. Wannan kuma shi ne ainifin abin da ake nufi da tsaftace kabila."
Dangane da Sudan kuma, wani da ake kira Emmanuel Jal, wanda tsofon soja ne, kuma a yanzu jakadan neman zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan, yayi suka ne da kakkausan harshe akan salon kamun ludayin shuagabannin Afurka game da zaman lafiyar yankin na yammacin kasar Sudan.
"Emmanuel Jal ya ce: Masu fada a ji a siyasar Afurka sun yi ko oho da makomarmu. A kodayaushe zaka tarar muna bakin kokarinmu wajen dora wa kasashen yammaci laifukan abubuwan dake faruwa. Abin da zan fada wa shuagabannin shi ne, kuna bau ta wa mulke-mulkenku na siyasa da makalewa da ofisoshinku kamar kaska, ba abin dake ci muku tuwo a kwarya a game da talakawan kasashenku. Kiran da nike wa kungiyar tarayyar Afurka shi ne ku yi wa gwamnatin Sudan matsin lamba ku kuma kara yawan sojoji domin kare lafiyar jama'a a Darfur."