Bude taron sauyin yanayi a Nairobin,Kenya | Labarai | DW | 06.11.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bude taron sauyin yanayi a Nairobin,Kenya

An bude taron sauyin yanayi wanda zai mayar da hankali wajen tallafawa kasashe matalauta,akarkashin jsagorancin mdd a Kenya.Wakilai daga sassa daban daban na duniya ke halartan taron,wanda ke zama irinsa na farko da aka gudanar a wata kasar Afrika dake kudu da sahara.A jajibirin wannan taro,dai mdd ta fitar da wani rahoto adangane da batutuwa da zaa tattauna,dangane da sauyin yanayi a wasu yankunan Afrika.Inda zaa samu koma baya a albarkatun gonaki,ayayinda tekuna zasu yi ambaliya zuwa cikin birane.Wannan taron na birnin Nairobi,wanda ke zama na 12 irinsa a karkashin jagorancin mdd,tun bayan rattaba hannu a yarjejeniyar sauyin yanayi a 1992,sai dai a makon daya gabata ne aka fitar da wani rahoto dake bayyana karuwar hayakin gas dake haddasa dumamar yanayi.

 • Kwanan wata 06.11.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu4x
 • Kwanan wata 06.11.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu4x