Bude taron Kungiyar Commonwealth a Kampala | Siyasa | DW | 23.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bude taron Kungiyar Commonwealth a Kampala

Wakilan gwamnatocin Kasashe 53 na Commonwealth ne ke halartan taron Uganda

default

Sarauniyar Ingila a bude taron Commonwealth a Kampala

A yau ne aka buɗe taron ƙungiyar ƙasashen renon Ingila ta Commonwealth a birnin Kampalan Uganda,inda shugabannin zasu tattauna matsalar sauyin yanayi,yini guda bayan dakatar da Pakistan daga ƙungiyar.

Duk da martanin ɓacin rai daga gwamnatin Islamabad ,da barazanar janyewarta daga wannan ƙungila,shugababbnin kasashen dake halartan taron sun kare dalilansu na ɗaukar wannan mataki.

Babban Sakataren ƙungiyar ta Commonwealth Don McKinnon,ya fadawa taron manema labaru cewar,sanin kowa ne kowace ƙasa aka dakatar daga wannan ungila,takan yi korafin cewar,bamu fahinci ainihin abunda ke tafiya a cikin ƙasar ba ne, a wannan lokaci.Amma a ga nina mun fahinta.

A ranar alhamis data gaba nedai,wa’adin da Commonwealth ta bawa Musharraf na ɗage takunkumin daya sanya wa ƙafofin yaɗa labaru,tare da tuɓe kakin soji domin ajiye mukamin sa na hafsan sojin Pakistan da sakin Alkalai da masu goyon bayan Jami’iyyun adawa dake tsare,ya cika.

Shugabanni da Priministocin ƙasashen ƙungiyar ta Commonweath din kaza lika zasu tattauna matsalar sauyin yanayi da duniya ke ciki a yanzu haka.

Shugaban jami’iyyar adawa ta MDC a ƙasar Zimbabwe Morgan Tsivangirai na daga cikin mahalrta taron na birnin Kampala,wanda yace yana Ugandan ne bisa gayyatar gabatar da bayanai,a bayan fagen wannan taron.To sai daya ke an dakatar da Zimbabwe daga wannan ungila ko yaya zuwan shugaban adawar zai shafi dangantakar Mugabe da shugaba Yuweri Museveni na Ugandan..”Kamar yadda na faɗa,ina son ka fahinci cewar idan da nazo jawabi wa taron shugabannin Commonwealth ne ,wata kila da zai shafi dangantakar waɗannan ƙasashe,amma ba zan yi wa taron jawabi ba,zan yi jawabi ne kaɗai a gaban taron bayan fage,sai sakon zuwa ga kasashen dake ƙungiyar Commonwealth ne.A tucani ne ina da ‘yanci, hulɗa da ƙasashen Commonwealth,a mayina na ɗan asalin ta”

Ƙasar ta Zimbabwe dai na cigaba da fuskantar rigingimu na siyasa da matsalolin tattalin arziki,inda shugabannin ƙasashen yankin kudancin Africa suka gudanar da taro a kasar Tanzania dangane da rikicin.Adangane da haka ne Morgan Tsivangirai yace..”Shugabannin kasashen kudancin Africa sun gudanar da taro na musamman a Tanzania,kuma sun cimma yarjejeniyar cewar,za’a iya warware rikicin kasar Zimbabwe ne ta hangar zama teburin tattaunawa tsakanin jami’iyyar dake mulki da ta Adawa”

Adangane da matsalar ta ɗumamar yanayi kuwa, Prime ministan Malta Lawrence Goziyace hakki ya rataya a wuyan dukkannin wakilan ƙasashen na ganin cewar an rage yawan hayakin iskar gas mai guba da wajen kashi 50 cikin 100,nan da shekarata 2050.Sai dai babu tabbacin cewar wakilan ƙasashe zasu amince da rattaba hannu akan wannan shri da Maltan ta gabatar,a karshen wannan taro da za’a rufe ranare lahadi.Dawa cikin ƙasashen da Britanian tayayiwa mulkin mallaka a baya dai,akwai waɗanda ke cikin jerin manyan ƙasashen dake fitar da mafi yawan hayaki mai guba na masana’antu.Daga cikinsu kuwa akwai ita Britanna,da Canada da Australia.

Prime ministan Britanna a birnin na Kampala ,yayi alkawarin inganta rayuwar miliyoyin yara banana dake ƙasashen Africa da Asia matalauta,ta hanyar samar musu kayayyakin rubutu da karatè.

Britanna dai na muradin shugabannin ƙasashe 53 dake ƙungiyar ta Commonwealth dake halartan taron na Uganda,dasu bada goyon bayan su wa wannan manufa ta faɗaɗa harkokin ilimi way ara kimanin million 30 da basu da sukunin shiga makarantun primare ,a matalautan ƙasashen na Commonwealth.

Gwamnatin na Gordon Brown ta kuma yi alkawarin kashe dala million 218,domin ilimantar da yara million 7 dake fama da karancin ilimi a Nigeria.

Kaza lika Britanian zata kashe pam million 50 cikin shekaru 3 masu gabatowa,wajen ɗaukar nauyin scholarship na yara zuwa jami’o,tare da tallafawa ɗalibai 2,500 da masu bincike,a kasashen na Commonwealth.

Ƙasashen dake da wakilci a ƙungiyar da Britanian tayi wa mulkin mallaka dai sun haɗar da na yankin Africa da Asia da Carribean.