1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude iyakar Nijar da Najeriya, farin cikin 'yan kasuwa

Gazali Abdou Tasawa M. Ahiwa
March 22, 2024

A Nijar 'yan kasuwa da masu yaki da tsadar rayuwa sun ce sun gamsu da matakin bude iyakar kasar da Najeriya, bodar da ta ci gaba da kasancewa a rufe mako daya bayan Najeriya ta bude tata.

https://p.dw.com/p/4e28h
Kasuwar birnin Yamai
Hoto: AP

Tun a makon da ya gabata ne dai a wani matakin na mutunta umurnin kungiyar ECOWAS na cire wa Nijar takunkumin da aka saka mata bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023, Shugaban Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya ba da umurnin bude iyakar kasar tasa da makobciyarta Nijar mai tsawon kilomita dubu da 500, inda johohi hudu na Nijar din suka raba iyaka da jihohi bakwai na Najeriya.

To sai dai a tsawon mako daya hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar sun kin bude iyakar tasu da Najeriyar suna masu zargin Faransa da jibge sojoji a kan iyakar Najeriyar da nufin afka wa Nijar din.

Amma fa kiraye-kirayen da 'yan kasar na ciki da na waje suka yi ta yi ga hukumomin mulkin sojan Nijar na ganin sun tausaya wa talakawansu sun bude bodar ta Najeriya, sojojin sun ji wannan kira inda suka bai wa gwamnonin jihohi Diffa da Zinder da Maradi da Tahoua da kuma Dosso umrnin bude iyakar da misalin karfe 12 da minti daya na daren Juma'a.

Hada-hada a kasuwar birnin Yamai
Hada-hada a kasuwar birnin YamaiHoto: B.Hama/AFP/GettyImages

Su ma dai kungiyoyin yaki da tsadar rayuwa da kuma kare hakin kwastomomi a kasar na ganin matakin bude iyakar Najeriyar zai taimaka ga samar da wadatar kayan masarufi da kuma saukin farashi a kasuwanni.

Sai dai kuma hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar sun ki bude iyakar kasar da Jamhuriyar Benin, wannan kuwa duk da tasirin da tashar ruwan Cotonou da ke zama mafi kusa da kasar Nijar ke yi wajen shigo da kaya daga ketare ko fita da su zuwa waje.

‘Yanzu haka dai ‘yan Nijar na cike da fatan ganin mahukuntan kasashen biyu na Nijar da Benin za su samu fahimtar juna nan ba da jimawa da za tai ga bude iyakar kasashen biyu kamar yadda ta kasance a yau da Najeriya.