Buɗe taro kan makomar Afganistan a birnin London | Siyasa | DW | 28.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buɗe taro kan makomar Afganistan a birnin London

Ƙasashen Duniya zasu cigaba da taimakawa tabbatar da tsaro a Afganistan

default

Shugaba Hamid Karzai

A yau ne aka fara gudanar da taro akan makomar ƙasar Afganistan a birnin London inda ake sa rai cewa ƙasar ta yankin tsakiyar Asiya za ta miƙa buƙatar ƙarfafa haɗin-gwiwa tsakaninta da ƙasashe masu ba da agaji . Sai dai kuma ko shakka babu shugaba Hamid Karzai zai sha suka daga ƙasashe masu ba da taimako bisa zarginsa da suke yi da alhakin ba 'yan Taliban ƙwarin-gwiwa da kuma ƙaruwar cin hanci da rashawa a wannan ƙasa.

Taron na birnin London dai taro ne da gwamnatin ƙasar Afganistan ke daukar tamkar matakin inganta makomar wannan kasa da ma yankin ga baki daya. Bukatar gwamnatin Afganistan ne dai ita ce a dama da ita wajen duba makomar ƙasar inda alummar kasa ke fatan ganin cewa a karshe za a dauke su tamkar abokan aiki da ake damawa da su daidai wa daidai.Wannan itace bukatar da Shugaba Hamid Karzai zai gabatar a gun taron a baya ga shirin samar da zaman lafiya. Wahid Omar shine kakakin gwamnatin Afganistan . Ya bayyana muhimman bukatun gwamnatin kasar inda ya ke cewa......

Gurin gwamnatin Afganistan dai shi ne tabbatar da cewa an dauki dayan bangaren a matsayin bangaren da zai taka muhimmiyar rawa a fagen siyasa kasarmu. Kuma gurinmu shi ne sake hade yan Taliban da alumma , Ko shakka babu wannan abu ne dake bukatar hadin-gwiwa tsakanin kasashen wannan yanki

Wahid Omar Sprecher von Karzai

Wahid Omar kakakin Karzai

Tun wasu yan watanni da suka gabata ne dai kakakin gwamnain na Afganistan yayi kira da a shiga tattunawa a maimakon yaki tare da yin kira ga bukatar shigar da da yawa daga yan taliban. Gwamnatin Afganistan ta bukaci soke sunayan da yawa daga cikin shugabannin Taliban daga jerin yan taada da ake nema ruwa a jallo a Amirka. A baya ga haka shugaban na Afganistan zai bukaci yin tattaunawar gaskiya game da matsalar cin hanci da rashwa da ke addabar kasar.Akan haka Karzai ke cewa...

Yace gwamnatin kowace kasa na da nata matsala wajen tafiyar da mulki a fannin rikici da kuma cin hanci da rashawa. Saboda haka hakan na maanar cewa gwamnati kadai ce ke da ikon tafiyar da mulki.

Ko shakka babu a taron na birnin London Karzai zai sha suka daga akasarin masu zarginsa. Sai dai kuma zai bukaci kasashen da ke taimaka wa kasarsa da su dau kwararan matakai wajen tabbatar da tsaro a Afganistan. Kwararrun aikin soji a kasar ta Afganistan sun nunar da cewa kudin da ake kashewa akan sojan NATO guda a Afganistan a kowace shekara za a iya yin anfani da shi wajen horar da sojojin Afganistan guda 60 tare da kuma basu makamai. General Zaher Azimi kakakin maaikatar tsaron Afganistan yayi kira ga kasashen NATO da su sake yin nazari inda ya gabatar da bukatun gwamnatin Afganistan kamar haka...

A halin yanzu muna bukatar sojoji dubu 240 da kuma yan sanda dubu 160 Akan haka akwai bukatar samun tabbacin tallafin kudi cikin shekaru 20 masu zuwa.

Angela Merkel und Hamid Karzai Deutschland Berlin

Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel da Hamid Karzai,

Azimi yace da zaran a cimma wadannan bukatu dakarun kasa da kasa zasu ficewa daga Afganistan. To sai dai kuma an zura ido ana sauraoron ko shin Afganista zata iya mika wadannan bukatu nata a taron na birnin London. Rangin Dadfar Spanta shugaban tawwagar Afganistan a wannan taro ya kyauata fata game da haka yana mai cewa...

Ko kafin shiga wannan taro sai da muka tattauna tare da kasashen dake kawance da mu . Ina son ku sani cewa muna mutunta juna a akin hadin-gwiwar da muke yi da kasahen da ke kawance da mu

Mawallafiya: Halima Abbas

Edita: Zainab Mohammed