Buƙatar Amirka a Georgia | Siyasa | DW | 12.08.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buƙatar Amirka a Georgia

Arzikin mai da tura makaman yaƙi su ne buƙatun Amirka dangane da Georgia

default

Shugaban Georgia Mikheil Saakashvili

Gwamnatin Amirka ta yi kakkausan suka ga take-taken Rasha. Shugaba George W Bush ya yi kira da a gaggauta janye dakarun Rasha daga Georgia, amma gwamnatin fadar Kremlin ba ta kaɗu da haka ba. Shin mene ne na Amirka a cikin wannan rikici?


Ana iya kwatanta kalaman da ake ji yanzu da irin waɗanda aka saba ji a zamanin yaƙin cacar baka.


Muƙaddashin firaministan Rasha Ivanov ya kwatanta Georgia da wani kumbon leƙen asirin Amirka sannan shugaban ƙasa Mikhail Saakashvili a matsayin karen farautar Amirka.


Abin da ke akwai shine a cikin shekaru takwas da suka wuce babu ƙaƙƙautawa gwamnatin Amirka ta yi ta ba Georgia makamai da suka haɗa da tankokin yaƙi da rokoki da jiragen saman yaƙi da masu saukar ungulu da a jimilce kuɗinsu ya kai dala miliyan dubu ɗaya. Sannan shugaban Amirka George W Bush ya yi ta yabon shugaban Georgia Mikhail Saakashvili wanda ya taɓa karatun fannin aikin lauya a birnin New York kuma ya shafe lokaci mai tsawo yana yiwa wani kamfanin mai na Amirka aiki.


"Shugaba Saakashvili ya ƙuduri aniyar cike dukkan ƙa´idojin shiga ƙungiyar NATO."


Kalaman shugaba Bush ke nan a ziyarar da ya kai Georgia. Shugaban na Amirka ya fusata bayan NATO a taron ta na birnin Bukarest, ta yi watsi da shawarar da ya bayar na shigar da janhuriyar ta yankin Caucasus cikin ƙungiyar ƙawancen. Gwamnatin Amirka na mai ra´ayin cewa Georgia ƙasa ce mai muhimmanci wajen tura mai zuwa ƙasashen yamma kasancewar bututun mai daga yankin Baku na ƙasar Azerbaidjan ya ratsa cikin ta.


Duk da adawar da Rasha ta nuna an aiwatar da aikin shimfiɗa bututun man a Georgia, inji Sam Gardiner Ba´amirke masani kan harkokin Georgia da kuma dubarun yaƙi. Ya ce gwamnatin Amirka na tsoron cewa bututun man wanda aikin shimfiɗa shi ya ci kuɗi dala miliyan dubu 4 wanda kuma kamfanin mai na Amirka wato Chevron ya ke ciki, ka iya faɗawa hannun Rasha. Sannan ɗinbim arzikin mai da Allah Ya bawa yankin wani abin ne da Amirka ke sha´awar shi. Amma matakan sojin da Rasha ke ɗauka kan Georgia ka iya canza abubuwa nan ba da daɗewa ba. Sam Gardiner masani kan dubarun yaƙi ya ce kuskure yadda Amirka ta yi ta taimakawa gwamnatin Georgia da makaman yaƙi ido a rufe.


Ya ce: "Bisa wani babban kuskure Amirka ta sa gwamnatin Georgia ta yaudari kan ta, ta na ganin cewa ta na iya yin duk abin da ta ga dama a yankin kudancin Ossetia."


Yanzu kwantaragi tsakanin kamfanin Chevron da Georgia ya ƙare. Gwamnatin ta ce sojojinta za su kare bututun man idan buƙatar yin haka ta so. To sai dai ruwa ba sa´ar kwando ba ne domin sojojin Georgia ba su da ƙarfin tinkarar Rasha ko da kuwa an mayar da sojojin Georgia kimanin dubu biyu dake Iraqi zuwa gida kamar yadda Amirka ke son a yi cikin gaggawa.