1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Britaniya ta yi lale marhabun da sabuwar gwamnatin Nigeria

May 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuLL

Britaniya tsohuwar uwargijiyar tarayyar Nigeria ta yi alkawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sabuwar gwamnatin da aka zaɓa a Nigeria duk da zargin da aka yi na tafka maguɗi a zaɓen. Wannan bayanin na ƙunshe ne a cikin wata takarda da P/M Britaniya Tony Blair ya aikewa shugaban Nigeria mai barin gado Olusegun Obasanjo. Ofishin shugaban ƙasar ta Nigeria ya fidda wata sanarwa inda ya baiyana wani sashe na wasiƙar inda Blair ya yabawa nasarorin da Obasanjo ya samu. Bugu da ƙari wasiƙar tace Britaniya a shirye take ta yi aiki da Nigeria ta fannin aiwatar da sauye sauye da mulki na adalci na dimokraɗiya da kuma wanzar da cigaban rayuwar alúma. Ofsihin na Obasanjo yace Blair na fatan saduwa da Yar Aduá domin tattauna wasu fannonin ƙawance tsakanin Nigeria da Britaniya.