Britaniya ta sassauta fargaba a game shaánin tsaro | Labarai | DW | 05.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Britaniya ta sassauta fargaba a game shaánin tsaro

Sakatariyar alámuran cikin gidan Britaniya Jacqui Smith ta sanar da sassauta fargaba a game da barazanar tsaro ga Britaniya, daga ƙololuwa zuwa matsakaici, matakin da ake ciki kafin yunƙurin harin taáddancin da bai yi nasara ba a makon da ya gabata. Majoyoyi dake da kusaci da binciken yan sanda a game da harin na makon jiya a London da kuma Glasgow sun baiyana cewa dukkan mutanen takwas da aka kama sune jiga jigan waɗanda suka shirya harin. An baiyana cewa a ƙalla shida daga cikin su likitoci ne waɗanda suka haɗa da ɗan ƙasar Jordan da kuma ɗan Iraqi. P/M Britaniya Gordon Brown ya bada umarnin nazarin dokokin ɗaukar maáikatan jinya a asibitocin ƙasar mallakar gwamnati. Bugu da ƙari ya kuma bada shawarar kafa majalisar tsaro ta ƙasa wadda zata riƙa nazari akai akai a dangane da barazanar hare haren taáddanci.