Britaniya ta rage agaji wa Uganda | Siyasa | DW | 22.12.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Britaniya ta rage agaji wa Uganda

shugabaYoweri Museveni Uganda

shugabaYoweri Museveni Uganda

Gwamnatin Uganda ta zargi gwamnatocin kasashen ketare da suka hadar da Britania, da dakatar da agajin da suke bata ,saboda amfani da raayin ketare kan harkokin democradiyyan wannan kasa dake gabashin Afrika.

Britania dake zama kasa wadda tafi bawa Uganda agaji mai tsoka ta sanar da yanke yawan tallafin da kimanin Pounds million 15,kwatankwacin dalan Amurka million 26.5,tare da tsayar da wani tallafi na Million biyar a dangane da cafke shugaban adawa da wasu matsaloli na gwamnatin shugaba Yuweri Museveni na Uganda.

Wannan sanarwa daga Britani yazo ne kwanaki kalilan bayan gwamnatin Sweden ta sanar dad a dakatar da bada agajin kimanin dala million 8 ,daga cikin kasafin agajin da takan bawa Ugandan.

Gwamnatin Ugandan dai na gudanar da rabin harkokin tad a tallafin da take samu daga ketare.

To sai adai dai lokacin da suke tallfawa Ugandan,baki dayansu sun bayyana rashin amincewarsu da cafke Kizza Besigye dake jagorantar jammiyar adawa,da komowarsa daga gudun hijira a watan daya gabata.

Bugu da karti sun bayyana damuwansu a dangane da matsayin democaradiyya da makomarta a wannan kasa.

Mai shekaru 62 da haihuwa,Shugaba Yuweri Museveni dai ya jagoranci Uganda na tsawon shekaru 19 da suka gabata,kuma bisa dukkan alamu zai sake zarcewa akan wannan mukami nasa a zavben ranar 23 ga watan Febrairu ,sakamakon gyaran fuska da yan majalisa sukayiwa kundun tsarin mulkin kasar,wadda ta haramta masa sake neman wannan mukami nasa a karo na uku.

Ministan raya kasashen ketare na Britania Hilary Benn yace dukkan kasashen dake aiki kafada da kafada da kasarta ,na aiki ne bisa tafarkin rage radadi na talauci wa alummominsu,da shawo kann matsalolin rashawa kana a daya hannun kuma da darajawa hakkin dan adam.

A dangane da hakane ya jaddada cewa dukkan wata hulda da zasu tafiyar da Uganda nan gabas,zasu taallaka ne kann wadannan manufofi.

Yace wadannan kudade da zaa janye daga tallafawa Uganda,zaa karkatar dasu ne wajen ayyukan tallafi na MDD a arewacin Uganda,wadanda zasu shiga Asusun wannan hukuma,kana sai baya zaben watan febrairu ne za san yadda zaayi da sauran moillion biyar da aka dakatar dasu a yanzu.

Sanarwa daga karamin ofishin jakadancin Britania dake Kampala na nuni dacewa,wannan mataki da aka dauka ya biyo bayan halin da kasar ke ciki yanzu ne na take hakkin yan jarida, da hana sashin shari gudanar da ayyukanta ,musamman tun bayan cafke shugaban yan adawa Kizza Besigye.

To sai dai gwamnatin ugasnda ta zargi kasashe dake tallafa mata ta bin raayoyi na ketare dangane da halin da kasar ke ciki.

Ministan yada labaru James Nsaba Buturo yace zasu cigaba da tattaunawa da wadannan kasashe masu tallafa musu tare da gabatar da nasu matsayi da raayi.

 • Kwanan wata 22.12.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu37
 • Kwanan wata 22.12.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu37