1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Britania da Iran an tsare sojoji 15

Hukumomin Britania sun tabbatar dacewa suna tuntubar juna da hukumomin Iran ta hanyar diplomasiyya ,akokarinsu na ganin cewa an saki sojin ruwan kasar guda 15 dake tsare.Sakaren tsaro na kasar ta Britania Des Broeneya sanar da hakan.Ministan ya fadaw manema labaru cewa,gwamnati na iyakar kokarinta na ganin cewa an warware wannan matsala cikin gaggawa ta hanyar diplomasiyya.Ayau di ne kuma wasu dalibai kimanin su 200,suka gudanar da gangami mai muni a kofar ofishin jakadancin Britania dake birnin Tehran,a wani abunda suka bayyana rashin jin dadinsu dangane da yadda sojin Britaniyan suka shiga kogin Iran ba tare da izini ba.