1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bremen: Ba da kyauatar zaman lafiya.

November 30, 2005

A ran juma'a 25 ga watan Nuwamba ne aka bai wa wasu `yan Najeriya lambar girmamawa ta zaman lafiya a birnin Bremen. Gidauniyar na ta "Die Schwelle" ta nan Jamus ne ke ba da lambar a ko wace shekara. Su dai `yan Najeriyan, su ne Imam Nurayn Ashafa da Reverend james Wuye.

https://p.dw.com/p/BvUC
Bremen
BremenHoto: Scheller

A karshen makon da ya gabata ne aka yi wani bikin mika lambar girmamawa ga wasu mutane da suka nuna kwazo a fannonin daban-daban na inganta halin rayuwar dan Adam da wanzad da zaman lafiya a duniya. Gidauniyar nan ta „Die Schwelle“ ta nan Jamus ne ke ba da kyautar a ko wace shekara. An gudanad da bikin wannan shekarar ne a zauren karbar baki na ofishin magajin birnin Bremen da ke can arewacin Jamus. A cikin wadanda aka girmama da lambar yabon, har da shugabannin kungiyar nan ta Inter-Faith Mediation Center ta jihar Kaduna a tarayyar Najeriya, wato Imam Nurayni Ashafa da Reverend James Wuye, wadanda gidauniyar ta yi musu matukar yabo, saboda namijin kokarin da suke yi wajen sulhunta rikicin kabilanci da na addini a jihar ta Kaduna da kuma wasu jihohi kamarsu Plateau da Bauci da kuma sauran wasu wurare a tarayyar ta Najeriya.

Bayan bikin girmama su da aka yi a birnin na Bremen, na sami damar yin doguwar tattaunawa da Imam Ashafa da Reverend Wuye a kan aikinsu da manufofin da suka sanya a gaba da kuma tarihin yadda suka kafa wannan kungiyar ta Inter-Faith Mediation Center, har ta kai ga matsayin da take da shi yau na samun amincewar kafofi da dama a gamayyar kasa da kasa.

A cikin firar tamu dai, malama biyu sun bayyana mini cewa, tun 1995 ne suka kafa wannan kungiyar a birnin Kaduna. Tun daga wannan lokacin kuma, sun yi ta kokarin sulhunta rikice-rikicen addini da ke kunno kai tsakanin kirista da musulmi, a Najeriya, musamman ma dai a jihar Kaduna, inda a nan ne aka fi samun rukunan addinan biyu masu cudanya, a wasu lokutan kuma gwagwarmaya da juna.

Da can dai, Imam Ashafa da Reveren Wuye, dukkansu shugabanni ne na kungiyoyin `yan tsatsaurar ra’ayi na addinansu. Sun yi ta jagorancin tarzoma da dama da suka barke a jihar ta Kaduna. Amma tun da suka kafa kungiyar Inter-Faith Mediation Center din ne suka canza sheka, suka yi ta aikin sulhunta rikice-rikice tsakanin mabiya adddinan biyu, inda labarin nasarar da suke samu, ya yadu, har aka dinga gayyatarsu zuwa kasashen ketare don su dinga ba da lacca da kuma gabatad da makalai a tarukan bita kan batutuwan da suka shafi wanzad da zaman lafiya tsakanin al’ummai daban-daban.

A zahiri dai, a da can, dukkansu biyu, wato Revrend Wuye da Imam Ashafa, sun kwashi talalabiyarsu a wasu tashe-tashen hankullan da suka taka rawar gani wajen shiryawa. A daya daga cikin wadannan tarzoman ne Reverend ya yi asarar hannunsa. Kazalika, Imam Ashafa, shi ma ya yi asarar `yan uwansa guda biyu da shaihin malaminsa a tarzomar da aka yi a Kaduna a cikin shekara ta 2001. Ko wadannan al’amuran ba su sa sun koma ga bin tafarkin `yan tsatsaurar ra’ayi ba ?

Shi Reverend Wuye kuwa, ya ce da farko, sai da ya yi ta nuna shakku ga Imam Ashafa saboda bala’in kyama da ke zuciyarsa a wannan lokacin. A hankali ne dai, bayan wasu al’amura da suka wakana a rayuwarsa, Allah ya juya hankalinsa, har ya zamo mai neman sulhu da sasanta rikice-rikce, maimakon ci gaba da kasancewa mai bin tsatsaurar ra’ayi.

Game da lambar girmamawar da aka ba su a birnin Bremen kuma, ga irin ra’ayoyin da malaman suka bayyanar.

To Madallah. Sashen Hausa na gidan rediyon Deutsche Welle na taya malaman murna da wannan karrama su da aka yi a birn Bremen na nan Jamus. Kuma yana fatar za su sami karin nasara wajen sulhunta rikice-rikicen da ke barkewa tsakanin al’ummai daban-daban a cikin gida Najeriya da kuma a wasu yankuna na Afirka da na kasashen ketare.