BP ya cimma nasarar hana kwararar mai a tekun Amirka | Labarai | DW | 17.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

BP ya cimma nasarar hana kwararar mai a tekun Amirka

Obama ya yaba da matakin da BP ya cimma na tsaida kwarar mai tun watanni ukku a cikin tekun Amirka

default

Mai yana kwarara a Tekun Mexiko

Hannayen jarin kamfanin mai na BP ya tashi bayan samun labarin nasarar dakatar da malalar mai a yankin tekun Mexiko. A kasuwannin hannun jarin birnin London, hannun jarin kamfanin BP ya tashi da kashi biyar da ɗigo 5.

A jiya ne dai Injiniyoyin kamfanin na BP su ka samu nasarar hana tsiyayar ɗanyen man fetur dake malala a tekun na Mexico, nasara irin ta ta farko da suka samu cikin watanni ukku da aukuwan hatsarin dandamalin haƙan man da ke tekun na Mexiko a Amirka.

Matakin da kuma babban jami'in dake lura da aikin na kamfanin  BP Doug Suttles ya ce shine matakin farko na hana kwararan man. kimanin gangar ɗanyen mai dubu 35 zuwa 60 ne dai kamfanin ke hasara a duk rana, lamarin da ya haifar da kareyewar hannayen jarin kamfanin a watanni ukku na baya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi