An kai harin kunar bakin a Maiduguri
June 17, 2018Majiyoyin tsaro a birnin Maiduguri sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP cewa, dan kunar bakin wake ne ya tarwatsa kansa loakcin da al'ummar musulmi ke dawowa daga shagulgulan bikin Salla a daren ranar Asabar.
Hari na biyu kuma ya biyo baya mintoci kalilan bayan da maharan suka harba abun fashewa a taron jama'a da suka kawo dauki kan mutane da harin farko ya ritsa da su. Babu kungiyar da ta dau alhakin harin nan take, amma hukumomi na zargin kungiyar Boko Haram da kai harin.
Wannan harin shi ne mafi muni a baya-bayannan bayan harin kunar bakin wake a kasuwa da kuma masallaci ya kashe mutane 86 a garin Mubi na jihar Adamawa. Kungiyar Boko Haram ta jima tana ta'asa kan fararen hula a jihohin Arewa maso gabashin Najeriya da wasu jihohin arewacin kasar, abinda ya yi sanadiyyar raba dubban mutane da gidajensu.