Boren adawa da cin hanci a Najeriya | Siyasa | DW | 15.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Boren adawa da cin hanci a Najeriya

Daruruwan matasa da kungiyoyi yakin da cin hanci da rashawa ne suka yi zanga-zangar lumana tare da fara zaman dirshen a gaban majalisar dokoki don matsin lamba ga ‘yan majalisar da alkalai kan zargin satar dukiyar kasa

Masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawar da wasunsu suka wo tattaki daga jihohin Najeriyar dai, suna dauke da kwalaye da aka rubuta bukatunsu na ‘yan majalisar su bayyana kasafin kudinsu, domin jama’a su sani tare da gudanar da bincike a kan zarge-zarge na cin hanci darashawa. Ife Williams jigo ne a kungiyar yaki da cin hanci da zamba cikin aminci ta Najeriya kuma ya soki lamarin cin hanci da a yanzu ke kara bazuwa tsakanin wadannan hukumomi biyu. 

Masu zanga-zangar dai sun yanke shawarar yin zaman dirshi na sai baba ta gani, a gab da majalisar dokokin Najeriya domin tabbatar da an dauki mataki na samun biyan bukata ga korafe-korafen nasu. Hauwa’u Adam da aka sani da Mama Kano ta ce ba gudu ba ja da baya kan wannan manufar ta su. 

Akwai dai mutanen da suka wo tattaki daga jihohin Najeriya don nuna goyon baya da zanga-zangar, alal misali Comrade Ibrahim Sani Bello da ya yi takaka daga Jalingo na jihar Taraba zuwa Abuja, ya fadawa DW cewa dole fa sai yan kasa sun tashi tsaye don a ja birki ga wadanda ke rike da mukamai a kasar, kuma suke amfani da hakan wajen arzurta kansu da dukiyar jama'a.

Har zuwa lokacin da DW ke hada wannan rahoton, babu wani jami’in majalisar dokokin Najeriya da ya fito domin yi wa masu zanga-zangar bayani, abin da ke nuna alamun zaman dirshin na lokaci mai tsawo.