1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bore a Hungary

Zainab A MohammadSeptember 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5O

Alumomin kasar Hungary sun gudanar da zanga zanga mafi girma a birnin Budapest ,inda suke kira ga Primier Ferenc Gyurcsany na jammiyar socialist da yayi murabuas.Kimanin mutane dubu 40, nedai sukayi jerin gwano a kofar majalisar dokokin kasar a yau.A boren na yau dai ,babu yansandan kwantar da tarzoma da sukayi ta arangama da masu boren cikin makon daya gabata,wanda ya haddasa raunana mutane sama 250.Wannan bore dai ya fara ne ,tun bayan da jammiyar Socialist mai mulki ta amince da dacewa,tayi karya ne da batun tattalin arzikin kasar domin ta samu daman lashe zabe a watan Afrilun daya gabata.Ptemier Ferenc dai ya lashi takobin cigaba da kasancewa kann karagar mulki,tare da aiwatar da karin haraji ,da rage kudaden gudanarwa.Manazarta dai sunce akwai alamun cigabansa kann wannan mulki.Wannan bore na Hungary dai yazo ne adaidai lokacin da kasar Poland ke fama da rigingimu na siyasa,kana kasar Czech a daya hannu,ta gaza nada sabuwar gwamnati.