1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bore a birnin Al-Hoceïma na Maroko

Salissou Boukari
June 28, 2017

Akalla jami'an tsaron 'yan sanda 80 ne suka samu raunuka a 'yan kwanaki biyu na baya-bayan nan a birnin Al-Hoceïma na kasar Maroko sakamakon arangama tsakanin 'yan sandan da masu zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/2faWb
Sitzblockade von Arbeitslosen in Al Hoceima Morocco
Masu zanga-zanga a birnin Al-Hoceïma na kasar MarokoHoto: F.Bouhbouh

Ya zuwa wannan Laraba ba a samu adadin wadanda suka jikkata daga bangaran masu zanga-zangar ba, akasari dai masu zanga-zangar sun yi amfani da duwatsu ne wajen jifan 'yan sandan a cewar hukumomin yankin. 'Yan sandan da suka jikkata sun samun sallama daga asibiti a cewar hukumomin yankin. 

An dai gwabza kazamin fada ne tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga tun daga ranar karamar Sallah ta karshen Azumin watan Ramadan a birnin na Al-Hoceïma. Masu zanga-zangar na girgiza acewacin kasar ta Maroko ne tun yau da watanni takwas. A cewar masu zanga-zangar, jami'an tsaron ne suka toshe duk wata kafa tare da hana yin zanga-zanga, abun da ya haifar da dauki ba dadi mai tsananin gaske.