Boran sojoji a Cote d'Ivoire
January 6, 2017Talla
An ba da rahoton cewar an ji duriyar manyan makamai a birnin na biyu mafi girma na Cote d'Ivoire watau Bouake a kusa da barakin sojoji.Masu aiko da rahotanni sun ce tsofin sojojin wadanda suka ce suna bukatar ko wane a bashi kusan Euro dubu bakwai da rabi na kudaden alawus da kuma gidan kwana,sun kai farmaki a kan wasu ofisoshin 'yan sanda guda biyu inda suka amshe makamai daga 'yan sandar wadanda suka tafi da su.