1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bomb ya ritsa da jirgin pasinja a India

November 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bub8

Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu ,kana wasu 60 sun samu raunuka sakamakon tashin wasu boma bomai guda biyu a jirgin kasa na Fasinjoji a jihar Bengal ta yamma dake India.Rahotanni daga kasar dai na nuni dacewa tarwatsewar boma boman ya raba wagogin jirgin biyu,wanda ya auku a kusa da kauyen Belakova.Jamian yansanda sunce wasu mutane sun makale acikin karafan jirgin .Duk dacewa har yanzu baa gano wadanda keda alhakin kai wannan harin ba,yansanda na zargin hannun kungiyoyin yan tawaye dake jihohin Bengal ta yamman da Assam.Harin na yau na mai zama na farkon irinsa a wannan jiha,tun daga shekara ta 1999,lokacinda bomb ya tarwatse acikin wani jirgin kasa dake dauki da jamian sojin Indian,akan hanyarsu zuwa Kashmir.A wancan harin sojoji 10 suka rasa rayukansu.