1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bomb ya kashe sojoji biyu a Mogadishu

June 28, 2007

Tashin bomb a yayi sanadiyyar mutuwan dakaru

https://p.dw.com/p/BtvC
Rigingimun Somalia
Rigingimun SomaliaHoto: AP

Wani Bomb da aka dasa a gefen hanya ya kashe sojojin guda biyo a birnin Mogadisho,dake zama fadar gwamnatin Somalia mai fama da rigingimu.

Wannan harin na yau dai ya auku ne saoi kalilan ne, bayan da wasu jamian agaji guda biyu suka rasa rayukansu a wani harin tsakar dare da aka kai musu a yankin arewacin kasar ta Somalia.

Wata mace data gane wa idanunta tashin bomb din na yau ,ta bayyana cewa motar dake dauke da dakarun ya tarwatse ,bayan sama da tashin bomb din yayi da ita,saboda tsananin sa,daga nan ne sai dakrun dake daya motar sintirin sojojin suka fara buda wuta da bindogoginsu.

Itama Halimo hussein dake zama daya daga cikin masu sayar da kayan abinci a kusa da inda harin ya auku,ta bayyana cewa ta ga gawawwakin sojoji guda biyu a zube a kasa bayan tashin bomb din.To sai dai kawo yanzu baa sanar da bangare da matattaun sojojin suka fito ba,tsakanin na gwamnatin rikon kwarya a Somalian,ko kuma na kasar Habasha dake taimaka musu.

A harin birnin Mogadishon yau dai fararen hula guda 4 ne suka jikkata,harin ke zama na baya bayannan daga cikin jerin rigingimu da wannan kasa ta somalia ke fama dasu,wanda kuma aka danganta da mayakan masu tsananin kishin addinin Islama dake fada da gawamnatin wucin gadin wannan kasa.

A harin na daren jiya dai jamian hukumar bada agaji wa marasa lafiya guda biyu ne suka rasa rayukansu a garin El-Berde ,mai tazarar km 480 daga arewa maso yammacin birnin na Mogadishu,dake zama fadar gwamnatin kasar.

Wani mazaunin yankin mai suna Adan Hussein,ya fadawa manema labaru cewa,jamii guda ya mutu nan take sakamakon harin,ayayinda gudan ya mutu ayayinda ake kokarin isa dashi asibiti domin jinya.

A yanzu haka dai gwamnatin wucin gadin wadda ke zama na 14 irinta a kasar ta somalia,na kokarin tabbatar da madafan iko a dukkan fadin kasar,abunda kuma ke neman cin tura.

Sanarwar data fito daga hukumar kula da yan gudun hijira ta mdd na nuni dacewa sama da mutane dubu 5 da dari 5 suke tsere daga birnin mogadishu,domin neman mafaka sakamakon karuwan tashe tashen hankula a cikin wannan wata na yuni kadai.

To sai dai a hannu guda kuma yan kasar dubu 123 kachal,daga cikin adadin dubu 401 da suka tsere daga birnin sakamakon cigaban rigingimu tsakanin watan febrairu da mayu ne suka komo gida,ayayinda kimanin mutane dubu 10 ne suka yi gudun hijira sakamakon fada tsakanin hauloli dake gaba da juna, ayankin tashan jirgin ruwannan na Kismayu.